Wata Sabuwa: Gwamnatin Jihar Zamfara Zata Dauki Bokaye 1,700 Don Samar Da Tsaro

161

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce zata dauki bokaye guda 1700 domin su yi yaki da rashin tsaro a jihar.

Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar, Alhaji Bello Dankande ya bayyana hakan a jiya laraba 4 ga watan Afrilu a lokacin da yake ganawa da sarakunan gargajiya da shugabannin Fulani a garin Gusau.

Alhaji Bello ya ce za a bukaci bokaye guda 100 daga kowanni masarautu guda 17 da ke jihar wanda zasu zama kari ne akan bokaye dari 500 da aka dauka daga masarautun a baya.

Haka zalika, zasu dauki mutane da zasu dinga gadin gidajen mai domin tabbatar da cewa yan bindigan ba su samu ba a dazukan da suke boye.

Da yake bayani akan yanayin tsaro a jihar, kwamishinan ya ce gwamnati ba zata sanya idanu tana kallo ana kashe mutane ba, don haka zata dauki kwararen matakai dan hana cigaba da faruwan hakan.

Ya kara da cewa, rundunar sojoji ta kasa ta kaddamar da Operation Harbin Kunama na Uku a jihar a ranar Litinin da ta gabata. Hakan ya nuna gwamnatin jiha da na tarayya na iya bakin kokarinsu don kawo karshen kashe-kashe a jihar.

A nashi bangaren sarkin Gusau, alhaji Ibrahim Bello ya ce zasu bada hadin kai, su yi aiki tare da gwamnati don a magance lamarin. Ya kara da cewa a matsayinsu na wakilan al’umma zasu ta ka muhimmiyar rawa wajen kawi karahen matsalar. Ya bada tabbacin bada hadin kan masarautu da masu ruwa da tsaki, da gwamnati, da jami’an tsaro don yaki da yan ta’addan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan