Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta bayyana irin ɓarnar da mahara suka yi a Kajuru

197

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da harin da aka kai a ƙayen Ungwan Aku dake ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna inda rahotanni suka ce an kashe mutum 20 ranar Litinin.

Mai magana da yawun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kadunan, Yakubu Sabo ya ce mutum 21 ne mahara suka kashe a ƙauyuka biyu a Kajuru ba mutum 20 ba kamar yadda aka bada rahoto tun da farko.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan ya ƙara da cewa ce mutum uku ne suka samu rauni sakamakon harbin bindiga a harin, yayin aka ƙona gidaje 10.

Mista Yakubu ya ce gaba da cewa haka kuma ‘yan bindigar sun sace shanu 50 a yayin wancan hari.

Ya ce ƙauyuka biyu maharan suka kai wa hari- Banono da Ungwan Aku dukkaninsu a ƙaramar hukumar Kajuru.

A cewarsa, wani gungun mutane ne da yawa ɗauke da makamai a kan babura suka kai hari a Banono da Ungwan Aku, inda suka yi ta harbin duk abinda suka ci karo da shi.

“Ranar 8/4/19, da misalin ƙarfe 9:30 na safe, muka samu kiran waya dake cewa wani gungun mutane ɗauke da makamai a kan babura sun shiga Banono da Ungwan Auku; duk ƙauyuka ne maƙobta dake lardin Kufana a ƙaramar hukumar Kajuru.

“Maharan suka fara harbi, suna kai wa mazauna ƙauyukan hari, a haka ne suka harba mutum ashirin da ɗaya (21), suka jikkata wasu mutane uku (3), suka kuma ƙona gidaje goma (10). Haka kuma, maharan sun sace kimanin shanu hamsin (50)”, Kakain Rundunar ‘Yan Sandan ya bayyana haka a cikin wata sanarwa ranar Talata.

Kakakin ya ƙara da cewa a lokacin harin, an tura ‘Yan Sandan Kwantar da Tarzoma, jami’an ‘yan sanda na yau da kullum, Sojoji da ‘yan ƙato da gora zuwa yankin, suka dakatar da harin, sannan suka kwashe waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti.

Ya ce ana nan ana ƙoƙarin cafke maharan dake shirin tserewa, ya ce an tura da ƙarin jami’an ‘yan sanda zuwa yankunan don kare faruwar harin ɗaukar fansa da kuma kiyaye doka da oda.

Ya bayyana ƙoƙarin da Rundunar ‘Yan Sandan ke yi ta hanyar Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Abdulrahm Ahmad na kama maharan tare da gurfanar da su a gaban kotu.

“Rundunar na kira ga jama’a da su ci gaba da taimakawa ‘yan sanda da bayanai masu muhimmanci waɗanda za su taimaka wajen magance waɗannan ƙalubale, a kuma iya kama waɗannan masu laifi”, in ji Mista Yakubu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan