An Ceto Mutum 136 Daga Kangin Bauta A Kasar Libya

298

Hukumar Bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta ce ta karbi yan Najeriya mutum 136 da suke samu kaansu cikin tagayyara a kasar Libya.

Shugaban tsare-tsare na yanki legasna hukumar NEMA, ALalhaji Idris Muhammad ne ya bayyanawa manewa labarai cewa mutaben sun sauka a babban tashar jirgin sama na Murtala Muhammad da ke lagas da misalin karfe 11:50 na daren litinin.

Alhaji Idris ya ce mutanen sun samu damar dawowa gida ta hannun kungiyoyin International Organisation for Migration (IOM), da European Union karkashin shirin Assissted Voluntary Returnees (AVR). Mutanen da aka maido sun hada da mata guda 59, da yara mata gufa hudu, da jarirai mata guda biyar. Sai maza gudab63, yara maza guda biyu da jarirai maza guda uku, hakan ya hada jumullar mutum 136.

Ya kara da cewa, hukumar NEMA da hukumomin National Refugees Commissiin, da National Agency for the Prohibition of Trafficking in Persons, da Nigeria Immigration Service ne suka karbi mutanen.

Daya daga cikin mutanen da suka dawo mai suna Kehinde Fatukasi dan jihar Ekiti ya zanta da manema labarai 8nda ya bayyana nadamarsa na yin wannan tafiya.

Mista Kehinde mai shekaru 42 ya ce, ya bar kasarnan a shekarar 2016, shi da matarsa, da dansu mai shekaru shida da niyyar zuwa kasar jamus don samun ingantaccen rayuwa amma sai suka fuskanci matsaloli da dama a kasar Nijar a lokacin da suke bi ta cikin sahara domin wucewa zuwa turai.

Ya kara da cewa duk da haka, basu hakura ba, sai suka wuce zuwa kasar Libya inda a nan ne aka sace su kuma aka sayar da su a matsayin bayi amma ba da dade wa ba sai matarsa ta samu ta kubuce kuma kungiyoyin agaji suka taimaka mata ta dawo gida.

A bangarensu, mista Kehinde da dansa suna tsare a hannun masu safarar mutane wanda suke gana musu azaba iri-iri. A gaban su ake sai da mutum ga masu siyan sassan jikin dan Adam. Ya ce, dayawa daga cikinsu ana sa su aiyuka na wahala kuma ba a biyansu, ga wulakanci da cin mutunci da ake musu.

Kuma duk wanda ya yi kokarin taurin kai, nan take ake kashe shi. Wahala da Azabar da suka fuskanta ya sa basa tsoron mutuwa domin akan idanunsu ake kashe mutane.

Ya kara da cewa yan Libya basu damu kai bakar fata ne ko balarabe , hatta yan uwansu larabawa yan kasashen Tunisia da Algeria tare ake hadasu ake azabtarwa ko a kashe.

A Karshe, mista Kehinde ya yiwa Allah godiya da ya basu ikon dawowa gida shi da dansa, kuma ya ce zai nemi matarsa wanda ya ke tunanin ta zaci sun mutu. Yana da burin yin noma domin ya kula da iyalinda su samu ingantaccen rayuwa a nan, duk da cewa ya wahala amma ya koyi nimq a kasar ta Libya kasancewarsu gwanaye wajen noma.

Sannan ya gargadi yyan kasa da su yi hakuri da yanayin da suka tsinci kansu a ciki, su nemi sana’a don inganta rayuwarsu, yafi su ce zasu tafi kasashen turai ta barauniyar hanya da zai iya zama sanadin ajalinsu

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan