Kasar Saudiyya Ta Ce Yan Najeriya 23 Ke Jiran Hukuncin Kisa

45

Kasar Saudiyya ta bayyana sunayen yan Najeriya da zasu fuskanci hukuncin Kisa a Kasar. Jakadan Masarautar saudiyya a kkasarnan Ambasada Mahmud Bostagi ya bayyana cewa an zartar da hukuncin akan mutane su 23 bayan an samu hujjoji da suka tabbatar da laifin da ake zarginsu da shi.

Ya ce kasar Saudiyya tana yanke wannan hukuncin ba don cin fuska ko wulakanci ba, sai don kare kasar kuma ana zartar da hukuncin bisa gaskiya da adalci bayan an samu hujjojin da suka tabbatar da laifin da ake zargi.

Ambasadan ya kara da cewa, akwai kimanin Yan Najeriya miliyan daya da dubu dari biyar da ke zaune lafiya a kasar ta Saudiyya ba tare da sun fuskanci wani muzgunawa ba. Don haka ya roki hukumomi a tashoshin jiragen saman kasarnan da su samar da tsare-tsare da zai hana fasa kwaurin miyagun kwayoyi.

Jerin sunayen mutanenguda 23 da aka bayyana masu jiran hukuncin kisa sune:
Adeniyi Adebayo Zikri, da Tunde Ibrahim, da Jimoh Idhola Lawal, da Idris Adewunmi Adepoju, da Lolo Babatunde, da Abdul Raimi Awela Ajibola, da Sulaiman Tunde, da Yusuf Makeen Ajiboye, da Adam Idris Abubakar, da Saka Zakariyya, da Biola Lawal, da Isa Abubakar Adam, Da Ibrahim Chiroma, da Hafis Amosu, da Aliyu Muhammad, da Ms Funmilayo Omoyemi Bishi, da Ms Mistura Yekini, da Amina Ajoke Alobi, da Kuburat Ibrahim, da Alaja Olufunke Alalaoe Abdulqadir, da Fawsat Balogun Alabi, da Aisha Muhammad Amira, da Adebayo Zakariya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan