Takarar Sanata Ali Ndume ta samu tazgaro domin kuwa Gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno, wanda ya fito daga jiha ɗaya da Sanata Ndumen ya ce duk da cewa jiha ɗaya ya fito da Sanata Ali Ndume, ba zai yi watsi da zaɓin da jam’iyyar APC ta yi wa Sanata Ahmad Lawan ba a matsayin ɗan takararta idan an zo zaɓen Shugaban Majalisar Dattijai.
Sanata Lawan da Sanata Ndume su ne manya-manyan ‘yan takarar Shugaban Majalisar Dattijai.
Sanata Ndume ya fito ne daga jihar Borno, yayin da Sanata Lawan ya fito daga jihar Yobe, maƙobciyar jihar Borno.
Gwamna Shettima ya bayyana matsayin nasa a gidansa na Abuja lokacin da Ƙungiyar Tallafawa Takarar Sanata Ahmad Lawan ta kai masa ziyarar girmamawa.
Ya ce a matsayinsa na mai biyayya ga jam’iyya, ya zaɓi ya yi biyayya ga hukuncin da jam’iyyar ta ɗauka.
Gwamna Shettima ya ce mafi yawa daga cikin ‘yan jam’iyyar APC, musamman daga Arewa sun ci zaɓe ne sakamakon alaƙanta kansu da suka yi da Shugaba Muhammadu Buhari, saboda haka bai kamata su ƙi bin zaɓin jam’iyyar ba.
“Ni ne lamba ɗaya na jihar, kuma na tuntuɓi jagororinmu daga Borno kafin in yanke shawarar goyon bayan Santa Ahmad Lawan.
“Abu mafi muhimmanci, ya kamata mu faɗi gaskiya. Muhammadu Buhari shi kaɗai ne ɗan takara a ƙasar nan wanda da yawa daga cikinmu muka ci zaɓukanmu sakamakon dangantaka kanmu da shi.
“Jiha ɗaya na fito da Mai Girma, Sanata Ali Ndume, kuma na amince da cewa gaskiya ne siyasa ‘yar gida ce. Amma kuma siyasa abu ce ta ƙasa.
“Na yadda cewa jinin da ya haɗa mu tare ya wuce duk wani abinda za mu yi hanƙoron nema.
“Amma ina tare da zaɓin jami’yyata, kuma in Allah Ya yadda za mu zaburar da duk waɗanda muke tare da su, don mu tabbatar da cewa muna tare”, in ji Gwamna Shettima.
Gwamnan, wanda shi ma sabon sanata ne da zai je Majalisar Dattijai ta 9, ya ce akwai buƙatar ‘yan jam’iyyar APC su ci gaba da yin ɗa’a ga jam’iyyar, ta hanyar girmama zaɓin jam’iyyar.
Ya ce hakan wajibi ne saboda babu wani tanadin ‘yan takara masu zaman kansu a litattafan doka.
“Sanata Ahmad Lawan muke goyon baya. Muna goyon bayan Femi Gbajabiamia da dukkan sauran sanatoci da sauran ‘yan Majalisun Wakilai da jam’iyyar take mara wa baya.
“Muna goyon bayan jam’iyyar da ta ba kowa damar yin takarar kowane ofishin siyasa. Mun yadda cewa dole mu girmama jam’iyya.
“Babu wani tanadin ‘yan takara masu zaman kansu, ban sani ba ko akwai wanda ya ci zaɓe ƙarƙashin tuta mai zaman kanta, wata ƙila sai dai sabon sanata, Ifeanyi Ubah wanda ya zo da jam’iyyar da ba a santa ba kuma ya ci zaɓe.
“To, na ji daɗin wannan ziyara, amma, a gaskiya wannan ziyarar ba a buƙatar ta. Ina tare da ku sosai. Ina goyon bayan Sanata Ahmad Lawan a matsayin Shugaban Majalisar Dattijai”, in ji shi.
“Shugaba Buhari ya goyi bayan takarar wasu daga cikin mafiya ƙwazon ‘yan takara da muke da su a a tsarin nan, da kuma inda muka fito. Sanata Ahmad Lawan ɗaya ne daga cikin mafiya ƙwazon ‘yan siyasa da muke da su. Abu ne a zahiri”, a kalaman Gwamna Shettima.
Ya ƙara da cewa Sanata Lawan ya kasance a Majalisar Dokoki ta Ƙasa tun 1999, saboda haka yana da gogewar da ake buƙata wajen tafiyar da Majalisa.
Gwamna Shettima ya ce ba yaƙi suke ba, ya ce shi da sauran zaɓaɓɓun ‘yan siyasar Borno za su ci gaba da rarrashin Sanata Ndume da ya haƙura da takararsa.
“Garinmu ɗaya, amma za mu ci gaba da rarrashin sa ya bi abinda jam’iyya ke so.
“Ba yaƙi muke yi ba. Tushenmu ɗaya”, in ji shi.
Sanata Ndume dai ya dage bisa takararsa ta Shugaban Majalisar Dattijai, duk da matsayin jam’iyyar APC, wadda ta fito fili ta goyi bayan Sanata Lawan.
Sanata Ndume ya soki matsayin na jam’iyyar APC, yana mai cewa abin ya saɓa wa dimukoraɗiyya, kuma an ɗauki matakin ne ba tare da tuntuɓa ba. Ya ce yana da goyon bayan da yawa daga sabbin sanatoci, har da na APC.