Shugaba Buhari Ya Jajantawa Kasar Faransa Bisa Gobarar Notre Dame Cathedral

136

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da dunbun jama’ar kasar bisa iftala’in gobarar da ya afku na cocin Notre Dame Cathedral a garin Paris.

Cocin mai dinbin tarihi wanda aka gama gininsa a shekarar 1435 ya kama da wuta a ranar litinin, 15 ga watan Aprilu, kuma hakan ya yi sanadin lalacewar wasu bangarori na cocin.

Shugaba Buhari ya nuna alhininsa na gobarar a cikin wata sanarwa da mataimakinsa na musamman akan harkokin yada labarai, malam Garba Shehu ya fitar.

A cikin sanarwan, ya jajantawa mabiya addinin kirista na kasarnan, da na duniya baki daya bisa lalacewar cocin mai tarihi wanda ya ke dauke da ababen tarihi da mabiya addinin suka dauke suka dauke su da muhimmanci.

Shugaban kasar ya kara da cewa, shi da daukacin yan kasarnan sun tsinci kansu cikin gigita da takaici bisa faruwar wannan gobara a wuri mai dauke da dimbim tarihi da daraha, kuma suna fatan Allah zai bada ikon da za a gyara shi kamar da.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan