Ƙungiyar Masu Ruwa da Tsaki ta Arewa Maso Gabas ta bayyana wanda take so ya yi takarar Shugaban Majalisar Dattijai

194

A ranar Alhamis ne Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa Maso Gabas da sauran ƙungiyoyi biyar dake shiyyar siyasar suka bayyana goyon bayansu ga Sanata Danjuma Goje don yin takarar Shugaban Majalisar Dattijai.

Da suke tashi daga wani taron gaggawa da suka yi a Zaranda Hotel dake Jihar Bauchi, ƙungiyoyin da suke haɗa da North East Elders Mobilisation Forum, APC National Youth Caucus, Borno Discussion Circle, Gombe Political Associations da North East Youth Awareness for Good Governance sun roƙi Mista Goje da ya fito ya bayyana takararsa cikin gaggawa.

Ƙungiyoyin, bayan duba na tsanaki da suka yi wa ‘yan takara uku daga Arewa dake neman muƙamin Shugaban Majalisar Dattijai, sun amince da Mista Goje, tsohon Gwamnan Jihar Gombe da ya yi takarar.

Dukkan jihohi shida da suke a Shiyya Siyasa ta Arewa Maso Gabas sun samu halartar taron tattaunawar.

Ƙungiyoyin sun kuma sanar da Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Kwamared Adams Oshimohole a rubuce bisa wannan amincewa tasu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan