Dubun wasu ‘yan fashi ‘yan Najeriya a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta cika

12

An yanke wa ‘yan Najeriya su takwas, dukkaninsu maza hukuncin kisa a Sharjah dake Haɗaɗdiyar Daular Larabawa, UAE, bisa samun su da laifin fashi da makami a cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗen ƙasashen waje da injinan ATM a watan Disamban 2016.

Ɗan Najeriya na tara da aka samu da kuɗin sata an yanke masa hukuncin zama gidan yari na wata shida.

Za a dawo da shi Najeriya bayan ya gama zaman gidan yarin.

Jaridar Gulf News ta ce ɗan Najeriyar ya musanta laifin da ake zargin sa da shi, yana mai cewa ɗaya daga cikin ‘yan uwan waɗanda ake zargin ne ya ce ya tura masa Dh60,000 (Dirhami) zuwa wani asusun banki a Najeriya.

Jaridar Gulf News da Khaleej Times, jaridun cikin gida da suka bada rahoton yanke hukuncin ba su bada bayanin waɗannan ‘yan Najeriya da aka yanke wa hukunci ba.

Da farko dai an kama ‘yan Najeriya guda 20 bisa laifin kai wa jami’an tsaro hari a cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗen ƙasashen waje da injinan ATM a birnin Sharjah a 2016.

A cikin mutum 20 da ake zargi, an yanke wa guda tara hukunci. Wasu daga cikin waɗanda ake zargi sun amsa laifukansu, yayinda wasu suka musanta tuhumar da ake musu.

Mai Shari’a Majid Almuhairi na Kotun Hukunta Masu Manyan Laifuka dake Sharjah ne ya yanke hukuncin ranar Laraba.

Gungun ‘yan fashin su takwas sun kai wa motocin jami’an tsaro hari, sun kuma shiga kamfanoni da ƙarfi, suka razana suka kuma ci mutuncin ma’aikata da al’umma da makamai masu kaifi a wasu jeren fashi, uku daga cikin hare-haren an kai su ne a ranar ɗaya, ranar 18 ga watan Disamba, 2016.

Gungun ‘yan fashin, waɗanda sun ce Haɗaɗɗiyar Daular Larabawar ne bisa bizar ziyara an ce sun shirya sosai, sun kitsa yadda za su kai wa motocin jami’an tsaro dake dakon akwatinan kuɗi daga injinan ATM zuwa injinan ATM hare-hare, da kuma a ƙalla kasuwar hada-hadar kuɗaɗen waje guda ɗaya a Sharjah.

Fashin farko ya afku ne a ATM ɗin wani Bankin Kasuwanci dake Dubai a kan Titin Sarki Abdul’aziz inda suka sace Dh340,000.

Bayan kwana biyu kuma sai suka kai hari a Shagon Zamani na Al Safeer dake Al Nahda, inda suka yi awon gaba da Dh700,000, da kuma wani ATM ɗin a Muweilah, inda suka sace Dh710,000.

‘Yan sanda sun yi nasarar daƙile hari na huɗu a wani ofishin kasuwar hada-hadar kuɗaɗen ƙasashen wajen kusa da National Paints.

An kama masu laifin a lokacin da ya dace, amma ‘yan sanda sun tabbatar da cewa wani sashin kuɗin ne kaɗai aka iya ganowa, kusan Dh1.8m kawai aka iya dawo da su, saboda ‘yan fashin sun raba kuɗaɗen a tsakaninsu, sun kuma aika da su ƙasarsu.

An kai waɗanda ake zargin ne ma’ajiyar masu laifi tare da haɗin kan jami’an ‘yan sanda a Dubai, Ajman da Fujairah.

‘Yan fashin sukan yi ta’asar ne da rana lokacin da ake tsaka hada-hada idan tituna sun cika da mutane, abinda ke ƙara kawo ruɗani, kuma ya ba su damar tserewa.

A kowane hari, ‘yan fashin sukan gudu kafin ‘yan sanda su iso.

Amma ‘yan fashin ba su iya guje wa na’urorin ɗaukar hoto ta jami’an tsaro ba, kuma ‘yan sanda sun iya gane maharan ne ta hanyar hotunan da aka ɗauka a Gidan Hada-hadar Kuɗaɗen Ƙasashen Waje dake cikin Shagon na Zamani.

Fayan-fayan bidiyo sun nuna ‘yan fashin suna far ma jami’an tsaro, suna kwasar kuɗi, kuma a ɗaya daga cikin hare-haren ma sun yanki hannun wani jami’in tsaro da wuƙa, kafin su gudu da akwatinan kuɗi.

‘Yan sanda sun yi imani cewa ‘yan fashin sun riƙa bibiya tare da bin sawun yadda ake amfani da motocin tsaro da ake jigilar kuɗi da su kafin aiwatar da hare-haren nasu.

Wani ɗan sanda ya shaida wa jaridar Gulf News cewa bisa doka, duk wani gungun mutane da suka razana jama’a tare da yin fashi za a yanke musu hukuncin kisa.

Amma ana sa ran ‘yan fashin za su ɗaukaka ƙara, daga nan kuma za a iya sassauta hukuncin zuwa ɗaurin rai da rai.

Wannan ƙara dai ba ta da dangantaka da kama wasu ‘yan Najeriya biyar da aka yi a watan Maris na bana, waɗanda suka yi wa wani mai kasuwar Canjin Kuɗaɗen Ƙasashen Waje fashin Dh2.3m (daidai da Miliyan 225.4) a Sharjah dake Dubai.

Waɗanda suka kai harin na watan Maris su ne Chimuanya Emmanuel Ozoh, Benjamin Nwachukwu Ajah, Kingsley Ikenna Ngoka, Tochukwu Leonard Alisi da Chile Micah Ndunagu.

Waɗannan ‘yan Najeriya su biyar sun kutsa zuwa Kasuwar Canjin Kuɗaɗen Ƙasashen Wajen ne, suka fasa gilashin dake tsakanin abokan ciniki da ma’aikatan Kasuwar ranar 20 ga watan Maris, suka sace kuɗaɗe na ƙasashe daban-daban, kuma suka gudu.

Ma’aikatan Kasuwar guda biyu sun samu raunuka sakamakon yunƙurin tare ‘yan fashin da suka yi.

Ɗaya daga cikinsu ne ya iya sanar da ‘yan sanda abinda ke faruwa.

Rundunar ‘Yan Sandan ta Sharjah ta haɗa kai da jami’an tsaro daga Abu Dhabi, Ras Alkaimah da Ajman daga jihohi huɗu cikin sa’o’i 48 bayan afkuwar harin.

Wani babban jami’in ɗan sanda ya ce waɗanda ‘yan fashi sun zo UAE ne bisa bizar ziyara ranar 18 ga watan Maris, 2019.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan