Bikin Easter: Mutane Goma Sun Rasu Yayin Da 30 Suka Jikkata A Gombe

118

Mutane goma sun rasa rayukansu, yayin da wasu 30 suka jikkata a lokacin da wata mota kirar Honda ta bi ta kan matasa mabiya Addinin Kirista da ke bikin Easter a daren lahadi a jihar Gombe.

Matasan, wanda suke gudanar da jerin gwanon tashin Yesu Almasihu daga matattu, hatsarin ya rutsa da mafi yawancinsu a lokacin da suke dai-dai Alheri junction, kan titin Biu, a cikin garin Gombe.

Shugaban kungiyar Boys Brigade na jihar, mista Isaac Kwadang ya bayyana wa manema labarai faruwar lamarin. Shugaban yace, a lokacin da matasan ke jerin gwanonsu, sai wani jami’in Civil Defence, da abokinsa Dan Sanda suka zo a mota, suka gaisa da matasan, sannan suka wuce gaban su kadan suka tsaida motar.

Suna tsaye a nan, har matasan suka zo suka wuce su, daga bisani sai wannan jami’i na Civil Defense ya kunna mota, tare da rakiyar abokin sa, sukayi kan matasa wanda hakan ya yi sandiyar mutuwar mutane da dama, yayin da wasu suka ji raunuka. Hakan ya harzuka matasan wanda, kuma nan ta ke, suka bi jami’an tsaron guda biyu har sai da suka cin musu, suka far musu har sai da suka ga basa numfashi.

Shugaban asibitin jihar Gombe, Dr. Shuaibu Mu’azu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace an kawo musu gawawwakin mutanen da suka rasa rayukan su sanadiyyar lamarin.

Shugaban Hukumar Kiyaye haddura ta kasa reshen jihar (FRSC), mista Godwin Omuko, ya tattauna da manema labarai kan faruwar lamarin, ya kuma tabbatar da hakan inda ya ce jami’ansu ne suka dauki gawawwakin zuwa asibiti.

A nasa bangaren, shugaban kungiyar kiristoci na yankin Arewa maso gabas, Dr. Abare Kala, ya yi kira ga mabiya addinin kirista da su yi hakuri, su dangana kada, su ce zasu dauki hukunci a hannunsu. Ya kara da cewa, yin hakan ba zai haifar da ďa mai ido ba, su bari Jami’an tsaro su dauki matakin da ya dace.

Mai magana da yawun Rundunar Yan Sandan jihar Mary Malun, ta ce mutum Goma ne suka rasa rayukan su, a ciki akwai matasa Takwas yayin da wasu 30 ke kwance a asibiti sai kuma jami’an Civil Defense da abokinsa Dan Sanda aka kashe.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan