Buhari ya nemi gudunmawar Qatar don inganta tattalin arziƙin Najeriya

351

A ranar Talata ne a Birnin Tarayya, Abuja Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga Qatar da ta zuba jari a ɓangarorin tattalin arziƙin Najeriya da suka haɗa da ɓangaren man fetur, wutar lantarki, sufurin jiragen sama, aikin gona da titin jirgin ƙasa don inganta rayuwar ‘yan Najeriya.

Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Kafafen Watsa Labarai, Femi Adesina ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar bayan wata tattarawar sirri tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al-thani a Fadar Gwamnati ranar Talata a Abuja.

Mista Adesina ya ce yana daga cikin abubuwan da suka mamaye tattaunawar tasu, batun dawo da Tafkin Cadi da ruwa daga Tafkin Kongo don kawo sauƙi ga rayuwar mutane sama da da miliyan 30 waɗanda ƙafewar Tafkin na Cadi ta shafa.

“Muna gayyatar ku da ku zuba jari a matatun man fetur ɗinmu, bututun man fetur, ɓangaren wutar lantarki, sufurin jiragen sama, aikin gona, ilimi da sauransu da dama, kuma ku samu waɗannan za su lura da yadda za a gudanar da zuba jarin. Muna buƙatar ƙwarewarku”, in ji Shugaba Buhari.

Game da Tafkin Cadi dake ƙafewa, Shugaba Buhari ya ce daga cikin mutane sama da miliyan 30 da abin ya shafa, fiye da rabi suna Najeriya ne.

“Muna buƙatar taimako wajen dawo da Tafkin Cadi, saboda ba aiki ne da ƙasashen da abin ya shafa za su iya yi su kaɗai ba.

“Dawo da Tafkin Cadin zai dawo da kamun kifi, noma, kiwon dabbobi, kuma tada ƙayar baya da shiga ƙasashe ba bisa ƙa’ida ba ba zai janye hankalin matasa ba.

“Muna son Qatar ta sa hannu saboda aikin jin ƙan ɗan Adam dake ciki”, in ji Shugaba Buhari.

Sheikh Hamad Al-thani ya ce ya yi farin cikin kasancewa a Najeriya a karon farko, yana mai nanata cewa ziyarar ta ramuwa ce bisa irin ta da Shugaba Buhari ya kai Qatar a shekara ta 2016.

“Dangantakar dake tsakanin ƙasashenmu tana da kyau sosai. Kawai sai dai mu ƙara gina ta”, in ji Sheikh Al-thani.

“Mun yi kamanceceniya a abubuwa daban-daban. Muna buƙatar inganta dangantakar kasuwanci da haɗin kan tattalin arziƙi.

“Muna son mu yi abubuwa da yawa tare da Najeriya, kuma za mu ci gaba da yin aiki bisa damammakin zuba jari don amfanin juna.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya ruwaito cewa Sarkin na Qatar, wanda ya kawo ziyarar aiki ta yini ɗaya zuwa Najeriya tuni ya koma Qatar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan