Masu satar mutane domin karbar kudin famsa, sun kashe wata baturiya yar Birrtaniya da wani dan kasar nan a wani wurin shakatawa a jihar kaduna,
Ofishin jakadancin birtaniya da ke kasar nan ne ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya bayyana sunan marigayiyar da Faye Mooney wadda ta ke yiwa wata kungiya aiki.
Kungiyar mai suna Mercy Corps ta bayyana cewa marigayiyar Faye Mooney na aiki a kasarnan kuma ta rasa ranta ne sanadiyyar wani farmaki da yan bindiga suka kai wurin da take hutunta a jihar Kaduna.
Rundunar Yan Sandan Jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, da yayin sandin mutuwar mutun biyu da kuma sace mutun wan da yan bindiga suka yi wanda ya auku a ranar jumua’a, 19 ga watan afrilu, shekaran nan.
Zuwa yanzu masu garkuwa da mutanen, sun kira waya, inda suka nemi kudin fansa har naira miliyan 60, kafin su saki mutunen da suka sace, amma Jami’an tsaro na iya bakin kokarinsu dan ceto su.