Akwai Yan Ta’adda Guda 10,000 A Jihar Zamfara Inji Gwamna Yari

224

Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya ce akwai akalla yan ta’adda da barayin shanu guda 10,000 a manyan sansani guda takwas a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a jiya alhamis 25, ga watan Afrilu a yayin da suke gudanar da taron akan tsaro a garin Gusau.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnati, Abdullahi Muhammad Shinkafi ya ce akwai kananan sansani guda 32 da yan ta’addan suke gudanar da muggan aiyukansu.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta gina cibiyoyin lafiya guda 715, da makarantun Firamare gida 570 amma aiyukan yan ta’addan ya hana al’umma amfana da su.

Aiyukan yan ta’adda, da satan shanu, da masu garkuwa da mutane don kudin fansa, ya dade yana damun al’umma kusan tsawon shekara Goma.

Yanzu haka, aikin yan ta’addan ya samu sabon salo wanda har sako suke turowa kafin su kawo hari, ba kamar a baya ba da sai dai a gansu.

Zuwa yanzu, kididdiga ya nuna cewa an kashe mutane 4,000, sannan mutane 100,000 sun yi hijira daga gidajensu, sai mata guda 8,000 da suka rasa mazajensu, da Yara 16,000 da suka zama marayu duka sanadiyyar mugun aikin yan ta’adda a jihar wanda ya shafi kowanni lungu da sako.

A karshe, gwamnan ya mika godiyarsa ga gwamnatin tarayya bisa kokarinta na hana aikin hakan ma’adanai a kokarinta na magance kashe-kashe da ya addabi jihar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan