Ko kun san limamai nawa Saudiyya za ta tura ƙasashen duniya don yin limanci a Ramadan?

239

Ministan Harkokin Addinin Musulunci, Da’awa da Shiryarwa na Saudiyya, Abdullatif Al-Asheikh ya amince da tura tawagar limamai 70 don su yi limancin sallar Asham da Tahajjudi a ƙasashe 70 a lokacin watan Ramadan.

Dama dai al’adar Ma’aikatar Harkokin Addinin Musulunci, Da’awa da Shiryarwa ne ta tura limamai ƙasashe don su ja salla su kuma wayar da kan Musulmi game da addinin Musulunci.

Al-Asheikh ya ce wannan yana daga saƙon Masarautar ta Saudiyya na kula da tallafa wa al’ummar Musulmi a ko’ina suke.

Ya ce limaman za su bayanin haƙiƙanin addinin Musulunci su kuma wayar da kan Musulmi game da ruƙo da ‘tsaka-tsakin’ ra’ayi a dukkan al’amura.

“An zaɓo limaman ne daga kwalejojin Shari’a. Sun san addinin sosai, kuma sun haddace Ƙur’ani”, in ji shi, yana mai ƙarawa da cewa: “Waɗannan matasan limamai sun iya wa’azi sosai, kuma za su iya yin bayanin addinin Musulunci sosai ga Musulmai”.

Ya ce yawanci masu ibada kan cika masallatai lokacin Ramadan, saboda haka wannan wata dama ce muhimmanci da limamai za su yi amfani da ita wajen yi wa Musulmai bayanai na shiryawa da wayar da kai.

Ministan ya tattauna da limaman ranar Litinin, ya kuma yi kira a gare su da su zama jakadun Masarautar na gari. Ma’aikatar ta shirya musu taron ƙarawa juna sani don ƙara wayar da su bisa hanyoyi da dabaru mafiya dacewa na yaɗa addinin Musulunci a ƙasashen waje.

Al-Asheikh ya kuma tattauna da manya-manyan jami’an Ma’aikatar ranar Lahadi game da aikace-aikacen Ma’aikatar lokacin Ramadan, Umara da aikin Haji.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan