Buhari ya umarci Malami da ya sa hannu wajen sakin Zainab Aliyu

237

Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, AGF, Abubakar Malami da ya sa hannu wajen sakin Zainab Aliyu, wata ɗaliba da aka yi kuskuren kamawa da laifin shigar da muggan ƙwayoyi a Saudiyya.

Hukumomin Saudiyya sun kama Zainab Aliyu, ɗaliba mai karatu a Jami’ar Maitama Sule dake Kano ne ranar 26 ga watan Disamba, 2018 bisa zargin ta da yin tafiya da jakar tafiya dake ƙunshe da muggan ƙwayoyi da ake zaton ƙwayar ‘tramadol’ ce.

Wadda ake zargin dai ta tashi zuwa Saudiyya ne don yin Umara ta Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Malam Aminu Kano tare da mahaifiyarta, Maryam da ‘yan uwanta, Hajara.

Mataimakiya ta Musamman ga Shugaban Ƙasa Kan Harkokin Ƙasashen Waje da Mazauna Ƙasashen Waje, Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana haka ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu, 2019, tana mai cewa tuni gwamnati ta fara ƙoƙarin ganin an sake ta, tare da wasu mutane biyu da ma suke cikin irin wannan hali.

” Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci AGF da ya ɗauki matakin da ya zama wajibi. Muna samun ci gaba mai kyau. Za ta dawo gida ita da wasu mutane biyu dake cikin irin wannan hali”, ta bada amsar haka ga wani mai amfani da shafin Twitter.

“Kowace ƙara tana da yadda ake gudanar da ita. Zainab ba ta yi wani laifi ba. Bai kamata a yi mata hukunci da laifin da ba ta aikata ba. Za mu tabbatar da an yi adalci kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya umarta”, ta ƙara da haka.

Wani ƙorafi da gidan su Zainab Aliyu suka shigar ne ya sa Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA ta yi bincike inda ta bankaɗo wasu ‘muggan mutane’ dake Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano waɗanda suka ƙware wajen jefa muggan ƙwayoyi a jakunkunan matafiya.

Kama mutum bakwai daga cikin muggan mutanen shi yasa aka gano cewa saka wa Zainab Aliyu ƙwaya ne a cikin jakarta ta tafiya ba tare da saninta ba.

“Bisa wannan bincike da aka gudanar, an gano cewa Zainab Habibu Aliyu ba ita ce mai jakar tafiya ta biyu da aka sa sunanta ba”, in ji wani rahoton NDLEA.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan