Ranar Ma’aikata ta Duniya: Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranar hutu

218

Gwamnatin Tarayya ta bayyana 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu don yin bikin Ranar Ma’aikata ta Duniya ta 2019.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdulrahman Dambazau, wanda ya bayyana ranar hutun a madadin Gwamnatin Tarayya ya yabi ma’aikatan ƙasar nan bisa jajircewarsu da sadaukarwa wajen gina kyakkyawar Najeriya.

Mista Dambazau, wanda laftanar janar ne mai ritaya ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka bayar a Abuja ranar Litinin wadda Georgina Ehuriah, Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ya fitar.

Ya yabi ƙoƙarin ma’aikata wajen tabbatar da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati ta hanyar aiki tuƙuru ga ‘yan Najeriya da ‘yan ƙasashen ƙetare.

Mista Dambazau ya yi kira da a ci gaba da samun goyon bayan ma’aikatan Najeriya wajen saita tattalin arziƙin ƙasar nan da kuma kai shi Mataki na Gaba.

Ya kuma yabe su bisa amincewa da suka yi da ƙoƙarin Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen gina kyakkyawar Najeriya.

Ministan ya taya ma’aikatan Najeriya Murnar Ranar Ma’aikata.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan