Rundunar Yan Sanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane A Jihar Kaduna

182

Rundunar Yan Sandan jihar Kaduna ta bayyana samun nasarar kama wani mutum mai suna Abubakar Ibrahim bisa zargin kashe basaraken kabilar Adara, Maiwada Galadima wanda aka yi harkuwa da shi kuma daga bisani aka kashe shi a watan Oktoban bara a karamar hukumar Kajuru.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa rawaito cewa mai magana da yawun rundunar Yan Sandana Kasa Frank Mba ne ya bayyana hakan a wani sanarwa da ya fitar inda ya ce an samun nasarar kama mutumin a ranar 15 ga watan Afrilu a Rigachikum, da ke karamar hukumar Igabi a garin Kaduna.

Bayan kama shi da Rundunar ta yi, ya furta cewa yana da hannunl a sace basaraken da kashe shi, da sauran sace-sacen mutane don karbar kudin fansa, da kashe-kashe a jihar Kaduna.

Baya ga haka, Rundunar ta samu nasarar cafke sauran abokan aikinsa da suka addabi jama’a. Gagaruman barayin da aka kama sun hadar da; Johnson Okafor mai shekari 44, da Shuaibu Iliyasu mai shekaru 20, da Ishaik Dabo mai shekaru 38, da Muhammad Nasiru mai shekaru 25, da Aminu Haruna mai shekaru 25, da Shafi’u Gudau mai shekaru 25, da Auwal Hamisu mai shekaru 24, da Ado Ya’u mai shekaru 35, da Ibrahim Yusuf mai shekaru 30, Ibrahim Audu mai shekaru 22, da Salisu Ajah mai shekaru 50, da Magaji Abubakar mai shekaru 27, sai Salisu Ali mai shekaru 18.

Bugu da kari, Rundunar ta samu nasarar cafke bokan da ke basu sa a domin aikata miyagun aiyukansu, mai suna malam Salisu Abubakar. A lokacin da aka yi kamen, an samu barayin dauke da bindigogi kirar AK47 guda 22, da kananan bindiga kirar pistol guda biyar, sai kuma alburusai da dama.

Mista Frank Mba ya rawaito shugaban Rundunar Yan Sanda na riko, Muhammad Adamu yana tabbatar da cewa zasu murkushe garkuwa da mutane da sauran miyagun aiyuka.

A farkon watannan ne shugaban Rundunar na riko, IGP Muhammad Adamu ya kaddamar da Operation Puff Adder domin yakar matsalolin tsaro musamman akan titin Kaduna zuwa Abuja.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan