Al’ummar Musulmi a ƙasashen Kudu Maso Yammacin Nahiyar Asia kamar Indonesia da Malaysia da yawancin Gabas ta Tsakiya kamar Misra, Iraƙi da Saudiyya sun tashi da azumin watan Ramadan yau Litinin, kamar yadda Kamfanin AP ya bayyana.
A ƙasashen Afrika ma, yau ne al’ummar Musulmi a Najeriya suka tashi da azumin watan na Ramadan.
Amma akwai yiwuwar miliyoyin al’ummar Musulmi a India, Pakistan da Iran za su tashi da azumin ne gobe Talata sakamakon rashin ganin wata a ƙasashen.
Musulmi suna amfani da tsarin ganin wata ne a kalandar Musulunci. Sakamakon haka, ba lallai ne dukkan ƙasashen Musulmi su fara azumi rana ɗaya ba.
A lokacin azumi, al’ummar Musulmi sukan yini ba ci ba sha, ba saduwa da iyali daga ketowar alfijir zuwa faɗuwar rana.
Haka kuma, Musulmi sukan duƙufa wajen yin ibadu kamar karatun Ƙur’ani, sallolin nafila, ciyarwa, sada zumunta da sauransu da niyyar samun kusanci da Ubangiji.