Majalisar Dokokin jihar kano ta kira wani zaman gaggawa a yau Litinin inda ta fara tattauna batun duba yiwuwar raba masarautar Kano zuwa masarautu hudu masu sarakunan yanka.
A yayin zaman da aka yi a litinin din nan, ‘yan majalisar dokokin sun tafka muhawara kan yadda suka ce, masarautar ta Kano tayi girman da ya kamata ace an raba masarautar ga wasu yankunan don kara inganta ayyukan masu rike da sarautun gargajiya dake matakin farko na hidimtuwar Alumma,

Haka kuma ‘yan majalisar da ke goyon bayan kudirin sun ce yin hakan zai kara bunkasa sauran yankunan da za’ a fitar musu da sarakuna masu cin gashin kansu suma.
Wakilinmu da ya halarci zaman yace masarautun da za’a kara a Kanon sun hadar da:
1-Masarautar Rano
2- Masarautar Gaya
3-Masarautar Bichi
4-Masarautar Karaye
Tuni Majalisar Dokokin ta Kano ta baiwa kwamitinta na kananan hukumomi da masarautu damar ya nazarci batun ya kuma gabatar mata cikakken rahoto gobe Talata don cigaba da bin matakan tabbatarda hakan.