Cibiyar aikin jarida ta hanyar zurfafa bincike ta Preminum Times ta shirya taron horaswa ga ‘yan jarida don sanin matakai da dabarun auna gaskiyar labari ta hanyar dorashi a mizanin tantancewa.
An dai fara gudanar da taron horaswar ne jiya Litinin a Otal din Tahir Guest Palace dake Kano, kuma zai gudana ne har zuwa Asabar din karshen makon da muke ciki.


A cewar jami’in cibiyar Mr Ogunleye, taron bitar ya samu tallafi daga kungiyar tarayyar Turai (EU) da British Cousil kuma su gudanar da makamantan wannan bitar a shiyyoyi uku ne na Arewacin kasar nan, ciki har da shiyyar Arewa maso yamma wanda jihar Kano take ciki.
A nasa jawabin Mr Babatunde, ya bayyana cewa sanin muhimmancin ‘yan jarida da aikinsu ne ya sanya su shirya taron horaswar, musamman la’akari da babban kalubalan dake akwai yayin gudanar da aikin jarida ta fannin zurfafa bincike.
Babatunde ya kuma jaddada irin illar da wallafa laburu marasa sahihanci ke haifarwa a cikin al’umma tare da zubar da kima da mutuncin ‘yan Jaridar, a don haka ne ya zama wajibi yayin gudanar da aikinsu su tabbatar da sahihancin labarun da suke watsawa cikin al’umma ta hanyar tabbatar da samun kwararan hujjoji a hannunsu.
Taron bitar ya samu halartar ‘yan jaridu daga kafafen yada labarai daban-daban na fadin jihar Kano da suka hadar da Radiyo da Talabijin da jarida tare da mawallafan kafar sadarwa ta zamani.
Turawa Abokai