Citad ta Karrama Matasan da Suka shiga Gasar da ta Shirya

171

A yau ne cibiyar fasahar sadarwa da cigaban al’umma (CITAD) ta mekawa wandansu matasa guda uku yan makarantun gaba da sakandire kyautar ladar cin gasar rubutu a kan yadda za a yaki cin hanci da rashawa wanda cibiyar ta kirkiro domin samar da mafita daga halin da kasar ta tsinci kanta.

Shugabar shirye-shirye ta sashen yaki da cin hancin ta CITAD Maryam Ado Haruna ce ta baiwa wanda suka samu damar lashe gasar ta wanan karo kyautar kudin yau a babban offishinsu da ke Jihar Kano.

Wadanda suka samu damar lashe gasar sun hada da Maimunat Abdulwab daga Jami’ar Ahmadu Bello ta zaria (ABU) da Offor Christopher daga Jami’ar UNN ta Nsukka, da kuma Na’ima Adamu ta shashin kula da muhali a Kano State Polytechnic.

Maryam ta bayyana rashin jin dadin ta bisa ganin yaddda matasa basu dauki  wannan gasa da muhimmanci ba, A cewar ta “yawancin wanda suka yi rubutun sun yi  kadan kuma basu bi ka’idar tsarin da ake bi ba wajen bada kyautar, duk da duba da lokacin da suke batawa a bisa yanar gizo wajen tsokaci akan rashawa amma basu yin kokari wajen rubuto hanyoyin magance aukuwar hakan ba.”

Kyautar 30,000 ce za a bawa na daya, na biyu 20,000 na uku kuma 10,000 amma a wannan karo ba wanda ya samu lashes kobo a dalilin rashin yawan shiga gasar, wannnan karon wadanda suka samu nasara an basu 10,000 ne kawai.   

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan