
Idan ana maganar gasar Europa league ta nahiyar turai to idan aka zo kan Unai Emery wato mai horas da Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a yanzu kamata yayi ace kurunkus.
Domin kuwa a tarihin gasar babu wanda ya raina gasar kamar Unai Emery, duba da yadda ya lashe kofin har sau uku kuma sau ukun ma a jere amma fa lokacin yana kungiyar kwallon kafa ta Sevilla.

Ga jerin shekarun da ya lashe kofin na Europa.
Ya lashe gasar a karon farko a 2014.
Ya lashe gasar karo na biyu a 2015.
Ya lashe gasar karo na uku a 2016.
Ga yadda Emery ya jagoranci Sevilla a dukkanin wasanni:
Emery ya jagoranci Sevilla a wasanni 205, ya lashe wasanni 105, yayi rashin nasara a wasanni 56, inda kuma ya buga kunnen doki a wasanni 44.
Amma fa kada a manta duk ya lashe wadannan kofuna a kungiyar kwallon kafa ta Sevilla dake kasar Spain.
Yanzu gashi ya sami nasarar zuwa wasan karshe karo na 4 a tarihin gasar bayan ya lallasa Valencia jimilla 7 da 4 gida da waje.

Shin Arsenal Sevilla ce? Ana ganin zai taimkawa Arsenal su kashe gasar karo na farko a tarihi?
Kowa yasan kalu-balen dake kan Arsenal idan har basu sami damar daukan wannan kofi ba, domin kuwa Arsenal zasu jefi tsuntsu 3 ne da dutse 1 ba tsuntsu 2 ba yayin buga wannan wasan karshen.
Ga jerin tsuntsayen da Arsenal zasu jefa:
- Idan har Arsenal suka lashe kofin Europa to hakan zaisa su sami damar samun tikitin buga gasar zakarun nahiyar turai.
- Arsenal basu taba lashe gasar Europa ba idan suka lashe sun kafa tarihi.
- Idan har Arsenal suka lashe gasar to su o,o zasu daina yimusu gori akan cewa basu da gasar Europa league ko gasar zakarun turai.
Amma matukar Arsenal suka gaza lashe wannan gasa ta Europa league to akwai matsala domin kuwa zasu rasa wadancan abubuwa uku da muka lissafa.
Arsenal zasu buga wasan karshe ne da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea wanda dukkannin su daga kasa daya suke kuma daga birnin London.

Shin ko Arsenal suna da saitin da zasu make tsuntsu 3 da dutse 1?