Arsenal zasu karawa Aubameyang da Lacazette kwantaragi

110

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dake kasar Ingila ta bayyana cewar zata kara tsawaita kwantaragin ‘yan wasan gabanta guda biyu wato Alexandre Lacazette da kuma Pierre-Emerick Aubameyang.

Hakan ya biyo bayan gudun mawar da wadannan ‘yan wasa suke bayar wa a kungiyar kwallon kafan musamman a gasar Europa league da ake yi a yanzu haka.

Wadannan ‘yan wasa sun taimkawa Arsenal wajen kaita Matakin wasan karshe da zasu fafata da Chelsea.

Hakan yasa Arsenal zata tsawaita kwantaraginsu ta dinga biyan ko wannensu albashin da yakai £250k a mako.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan