Ƙirƙirar sabbin masarautu: Sanusi ya yi murabus

264

Alhaji Haruna Rasheed Sanusi, Hakimin Ƙaramar Hukumar Bebeji dake Jihar Kano ya ajiye muƙaminsa.

Mista Sanusi ya bayyana haka ne a wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 5 ga watan Mayu, 2019.

Matakin nasa ya biyo bayan ƙirƙirar sabbin masarautu da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi.

Hakimin ya bayyana “dalilan rashin lafiya da canje-canjen da girma” a matsayin dalilan ajiye aikinsa.

“Bisa la’akari da dalilai na lafiya da kuma girma, haka zalika da yadda muka samu kanmu a yau, na dangane da yanayin da zamani ya zo mana da shi, na yanke shawarar ajiye jagorancin ƙasar Bebeji, daga yau Juma’a, 10 ga watan Mayu, 2019”, in ji wasiƙar.

A halin yanzu, Kano tana da masarautu biyar: Kano, Rano, Gaya, Ƙaraye da Bichi.

Dukkanin Sarakunan sabbin masarautun za su zama suna da iko iri ɗaya, kuma za su kasance a matsayin daraja ta ɗaya kamar Sanusi

Sabbin Sarakunan sun haɗa da Aminu Ado Bayero, ɗan marigayi, Sarkin Kano, Ado Bayero, wanda aka ba shi Sarkin Bichi.

Sarkin Gaya shi ne Alhaji Ibrahim Abdulkadir Gaya; Sarkin Rano shi ne Alhaji Tafida Abdulkadir Ila, yayinda Sarkin Ƙaraye shi ne Dakta Alhaji Ibrahim Abubakar II.

A halin yanzu, Masarautar Kano da Sanusi yake shugabanta tana da ƙananan hukumomi 10: Kano Municipal, Tarauni, Dala, Nassarawa, Fagge, Gwale, Kumbotso, Ungogo, Dawakin Kudu da Minjibir.

Masarautar Rano za ta yi iko da ƙananan hukumomin Rano, Bunkure, Kibiya, Takai, Sumaila, Kura, Doguwa, Tudun Wada, Ƙiru, Bebeji

Masarautar Gaya tana da ƙananan hukumomin Gaya, Ajingi, Albasu, Wudil, Garko, Warawa, Gezawa, Gabasawa.

Ƙananan hukumomin Ƙaraye, Rogo, Gwarzo, Kabo, Rimin Gado, Madobi da Garun Malam za su kasance ƙarƙashin Masarautar Ƙaraye.

Masarautar Bichi tana da ƙananan hukumomin Bichi, Ɓagwai, Shanono, Tsanyawa, Ƙunci, Makoɗa, Ɗanbatta, Dawakin Tofa da Tofa a ƙarƙashinta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan