Yadda Kanawa suka tari Sarki Sanusi II

196

Dubban mutane ne suka taru a Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Malam Aminu Kano dake Kano don raka Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II zuwa fadarsa.

Rahotanni sun ce Sarkin, wanda ya dawo daga Landan, yana fuskantar matsin lamba daga Gwamnatin Jihar Kano bisa zargin sa da goyon bayan ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP.

Dama tun da rana, wasu matasa ‘yan dabar siyasa da ake zargin masu yi wa Gwamnatin Jihar biyayya ne suka tarwatsa wani dandazon matasa waɗanda suka yi shirin yin tattaki zuwa filin jirgin saman.

Amma daga baya dai magoya bayan Sarkin suka shawo kan wannan barazana, inda suka ƙara tattaruwa don nuna soyayyarsu.

Sarkin dai ba ya ɗasawa da Gwamnan Jihar, wanda ya ƙirƙiri sabbin masarautu don rage masa tasiri.

Ranar Laraba ne Gwamna Ganduje ya sa hannu ga Dokar Masarautar Kano da ta Ƙananan Hukumomi, wadda ta bada damar ƙirƙirar sabbin masarautu a Kano.

Yayinda mutane suka tattaru don yin maraba da Sarkin, Gwamna Ganduje kuwa ya bijire wa umarnin kotu ne, inda ya bada Sandar Mulki ga ɗaya daga cikin sabbin sarakunan da aka naɗa, Sarkin Bichi, Aminu Ado Bayero.

A ranar Juma’a ne wata Babbar Kotun Jihar Kano mai zama a Ungogo ta umarci Gwamna Ganduje da ya dakatar da duk wani shiri na ƙirƙirar sabbin masarautun.

Ranar Asabar kuma Gwamnan ya ba sabbin sarakunan Takardun Kama Aiki, yana mai cewa ba shi da masaniya game da wancan umarni.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan