Majalisar Dattijai ta tabbatar da Emefiele a matsayin Gwamnan CBN

163

Majalisar Dattijai ta tabbatar da Godwin Emefiele a matsayin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN a wa’adin shugabanci na biyu.

Tabbatarwar ta biyo bayan miƙa sunansa da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a makon da ya gabata.

A ranar 9 ga watan Mayu ne Shugaba Buhari ya rubuta wasiƙa zuwa ga Majalisar Dattijai, inda ya sanar da su aniyarsa ta ƙara naɗa Mista Emefiele.

Shugaban ya bayyana a wasiƙar cewa wa’adin shugabanci Mista Emefiele zai ƙare ne ranar 2 ga watan Yuni, don haka ya nemi sahalewar Majalisar don ƙara naɗa shi, kamar yadda Sashi na 81 (2) na Dokar CBN ta 2017 ya nuna.

Ya ce sake naɗa Gwamnan na CBN zai kasance na wa’adin shugabanci na biyu, kuma na ƙarshe, na tsawon shekara biyar.

An naɗa Mista Emefiele ne a matsayin Gwamnan Babban Bankin a shekara ta 2014.

Bayan da Majalisar Dattijan ta karɓi wasiƙar ta Shugaban Ƙasa, sai ta miƙa tantance Mista Emefiele ga Kwamitinta na Banki, Kuɗi da Sauran Cibiyoyin Kuɗi.

Gwamnan Bankin da sauran sanatocin dake cikin Kwamitin sun kasance a cikin raha yayin tantancewar da aka gudanar ranar Laraba.

Da yake gabatar da rahoto ranar Alhamis, Shugaban Kwamitin, Rafiu Ibrahim (Kwara-PDP), ya ce Kwamitin ya gamsu da gogewar da Mista Emefiele ke da ita ta ‘fiye da shekara 30’.

Daga nan sai Kwamitin ya tabbatar da Mista Emefiele bisa ƙwazon da ya yi a wa’adin shugabanci na farko.

“Cewa mutumin da aka kawo sunansa ya fahimci yadda tattalin arziƙin ƙasar nan yake da faɗinsa, kuma ya yi amfani da ilimi wajen ci gaban da daidaituwar tattalin arziƙinmu.

“Cewa wanda aka kawo sunansa ya yi bajinta sosai a wa’adin shugabancinsa na farko, wadda ya sa ƙasar nan ta fita daga matsin tattalin arziƙi”, in ji Mista Ibrahim.

Tabbatarwar da shi ɗin ya samu amincewa ta hanyar murya, kuma dukkan sanatocin suka ce ‘ayes’, kalmar dake nuna amincewar kowa da kowa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan