Rashin tsaro: Gwamnonin Arewa sun bayyana matakin da za su ɗauka

227

Gwamnonin Jihohin Arewa 19 sun amince su gana da Shugaba Muhammadu Buhari bisa rashin tsaro dake addabar yankin.

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima ya bayyana haka ranar Juma’a lokacin da Gwamnonin suka gana a Jihar Kaduna.

A taron, wanda shi ne irinsa na farko a wannan shekarar, Gwamnonin sun amince su kafa Wata Cibiyar Kuɗi ta Haɗin Gwiwa wadda za ta magance matsalolin tattalin arziƙi a yankin, su kuma sa Cibiyar ta samu ‘yanci a ɓangaren kuɗi.

Gwamna Shettima a jawabinsa, ya ce kwanan nan Gwamnonin Arewa za su gana da Shugaba Muhammadu Buhari don yin musayar ra’ayi bisa yadda za a samu hanya mafi kyau ta shawo kan matsalar tsaro dake addabar yankin.

Yankin Arewan dai na fuskantar matsalolin arziƙi da sauran matsaloli da dama a shekarun da suka gabata wanda ya haɗa da Boko Haram, yawan garkuwa da mutane, faɗace-faɗace a ƙauyuka, rikici tsakanin manoma da makiyaya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan