Dalilin da yasa aka samu saɓani tsakanin Ganduje da Sarki Sanusi- Kwamishinan Yaɗa Labarai

231

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Kwamared Muhammad Garba ya bayyana dalilan da yasa Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya samu saɓani da Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II.

Ya kuma yi bayanin dalilin da yasa aka ƙirkiro sabbin masarautu a jihar a wata tattaunawa da ya yi da jaridar Sun.

Mista Garba ya ce Sarkin da ake ganin sa da ƙima ya shiga siyasa, abinda ya saɓa da al’adar kujerar da yake kai.

“Zahirin abinda ya faru a sakamakon ƙirƙirar sabbin masarautu, ya kamata ka tuna cewa ba gwamnati ce ta taso da batun kafa dokar ba. Wata ƙungiyar lauyoyi ce wadda ta ji cewa akwai buƙatar samun sabbin masarautu a yankinsu.

“Kuma suka rubuta wasiƙa zuwa ga Majalisar Dokoki ta Jihar Kano, Majalisar Dokokin Jihar kuma, daga bayanan da muke da su, sai ta karanta koken ko ma dai mene ne aka miƙa musu, kuma suka ji cewa dukkan batutuwan da waɗanda abin ya shafa da lauyoyin batutuwa ne masu muhimmanci waɗanda ya kamata a duba su.

“Majalisar Dokokin Jihar ta yanke shawarar yin aikin da Kundin Tsarin Mulki ya ɗora musu ta hanyar duba koken, suka ƙirƙiro doka, suka ɗan yi gyara ɗaya ko biyu, suka ci gaba kamar yadda Dokar Majalisar take. A ƙarshen karatu na uku, suka gabatar da ita ga Gwamna.

“Idan za ka iya tuna abinda Kakakin Majalisar ya faɗa lokacin da suka gabatar da wannan doka ga Gwamna Jiha, ya ce sun sun yadda da dokar sosai, da a ce Gwamnan ya ƙi ya rattaba hannu, da sai su dawo Majalisar su yi amfani da kaso biyu bisa uku su zartar da dokar, abinda yake nufin Majalisar ta gama gamsuwa.

“Kuma suka zo Gidan Gwamnati, suka yi mana jawabi, kuma Gwamna ya yi wa dokar kallon tsanaki, kuma muka ji cewa hakan shi ne abinda al’ummar Kano suke so, waɗanda ke rayuwa a wasu daga cikin waɗannan ƙananan hukumomi da ƙauyuka, muka ji cewa wani abu ne da zai bunƙasa waɗannan yankuna, duba da wasu daga ƙananan hukumomi a jihohin dake maƙobta da mu kamar Jigawa- kalli Masarautar Ringim misali.

“Na tuna lokacin da Kano take haɗe da Jihar Jigawa, Dutse ƙungurmin ƙauye ne. Na san Dutse a lokacin saboda na yi makaranta a Sumaila.

“Babu wuta, babu komai a Dutse. Amma lokacin da Dutse ta zama masarsuta, daga bisani kuma ta zama jiha, kalli irin matakin ci gaba da suka kai!

“Dubi ƙirƙirar Ringim, wadda ita ce masarauta ta ƙarshe da aka ƙirƙira. Je ka Ringim yau ka ga matakin ci gaba.

“To, lokacin da marigayi Abubakar Rimi ya yi yunƙurin samar da waɗannan masarautu a 1981/82, da an yadda an kafa waɗanda masarautu, musamman masarautu uku na Gaya, Ƙaraye da ɗayar, da an kafa su a wancan lokacin, ka yadda da ni, da zuwa yanzu, ta fuskar ci gaba, za ka yi mamaki sosai.

“Wani ɓangaren da muka duba shi ne ƙalubalan yau. Kuma muka dubi yankimmu, da kuma matakin rashin tsaro da Najeriya ke fuskanta.

“Mun karanta a jaridu, mun ji daga hukumomin tsaro cewa mafi yawa daga masu kashe-kashe, da yawansu sun dawo Kano.

“Kuma, mun san cewa sarakunan gargajiya suna da kyakkyawar rawar takawa wajen kula da zirga-zirga, mutane da sauransu.

“Kuma muka ji cewa don a samu cikakken tsarin kula da mutane, akwai buƙatar mu tabbatar da cewa mun samu cibiyoyin gargajiya da suke kusa da jama’a, fiye da abinda ake da shi a tsarin masarauta ɗaya.

“Gwamnan ya duba haka, da kuma batun yadda za su iya ba shi shawara wajen ci gaba, samar da hanyoyi, ta fuskar samar da ruwa, ta fuskar samar da ilimi, muna baya a harkar ilimi.

“Yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Kano abin tashin hankali ne sosai. Kuma muka ji cewa waɗannan sarakunan gargajiyar suna da babbar rawar da za su taka.

“Maganar gaskiya, mun dubu alfanun samar da waɗannan masarautu, kuma muka ji cewa babu dalilin ɓata lokaci. Saboda haka, sai Gwamnan ya rattaba hannu.

“Amma, abin kaico, lokacin da ake ƙoƙarin tabbatar da haka, sai wasu mutane suka ji cewa babu buƙatar a raba, wasu mutane suka ji cewa akwai wata matsala ta ƙashin kai ko wata matsala ta siyasa tsakanin Sarkin Kano da Gwamnan Kano.

“Sarki a matsayinsa na ɗan Adam, yana da damar zaɓi.

“Duba da muƙamin da yake riƙe da shi, dole ya kula bisa duk abubuwan da yake yi saboda shi yanzu uban kowa ne. Shugaban addini ne shi, kuma shi yanzu shugaban al’umma ne.

“Inda aka samu matsala, ko tsakanin Gwamna ne da wasu muhimman mutane a jihar, Sarki ake sa ran ya gayyace su ya sasanta.

“Haka ake nufi idan ka zama uban kowa. Amma a lokacin da Sarki ya zama ya shiga siyasa, siyasa sosai, ina jin wannan ita ce matsalar.

“Amma ba ma ganin sa ta wannan hanyar, kuma wannan ba shi ne ma dalilin ba. Ci gaban jihar shi ne ya dame mu.

“Maganar gaskiya, siyasar da ya shiga ma ba ta yi wata ma’ana ba, saboda duk da siyasar da ya shiga, mun iya cin zaɓe.

“Kuma, bayan cin zaɓe, Gwamnan bai yi farin ciki ba, saboda ba dalilin da Sarki zai yaƙe shi a siyasance.

“Dalili shi ne, dangantakar su ta kasance mai kyau sosai. Bai taɓa ba da wata shawara guda ɗaya wadda Gwamnan ya ƙi aiwatarwa ba.

“Gwamnan ya ji cewa idan akwai wata matsala, idan akwai wani rikici, idan akwai wani waje da Sarkin yake son a yi canje-canje, ta fuskar shawara, yana da hanyoyi da dama.

“Gwamnan yana girmama shi sosai. Duk lokacin da Sarkin ya zo Gidan Gwamnati, Gwamnan zai raka shi har wajen motarsa. Idan ya zo wajen wani taro a makare, Sarkin zai je kafin Gwamna.

“Amma a yawancin lokuta, Gwamnan yakan riga Sarkin zuwa. Kuma duk lokacin da ya zo, Gwamnan zai miƙe tsaye ya gaishe shi.

“Mu a iya sanin mu, duk abinda ya kamata a ba Sarkin a matsayinsa na uba an ba shi.

“Har bayan zaɓe, duk da mun san cewa wannan mutumin ya yaƙe mu da gaske, Gwamnan ya ci gaba da tafiya da shi.

“Ya je Fadar har sau biyu. A lokacin da aka ce mana cewa ba ya iya gudanar da aiki, Gwamnan ya je can a ƙashin kai.

“Ya kuma je don wata addu’ar zaman lafiya, ya je don ɗaura auren ma’aurata 1500. Gwamnan ya manta da siyasar da Sarkin ya yi.

“A iya sanin mu, ba mu yi haka (ƙirƙirar sabbin masarautu) don lalata tarihi ko wata wasiyya ko duk wani abu da kakannin-kakannin waɗannan Sarakunan suka kafa ba.
“Muna son abin ya kafu sosai. Muna son cewa a sa gidajen sarautar wajen tafiyar da jihar nan”, in ji Mista Garba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan