Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abudullahi Umar Ganduje ya tattara hujjojin da zai kare kansa da su a gaban Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓe ta Jihar Kano.
Gwamnan ya shirya mujalladai biyar na hujjoji masu shafi 1800, zai kuma gabatar da shaidu 203 waɗanda za su faɗa wa duniya cewa an yi zaɓe na adalci ranar 23 ga watan Maris, 2019.
Lauyan Gwamnan, Barista Musa Abdullahi Lawan ya bayyana haka ranar Asabar.
Mista Lawan ya yi wannan jawabin ne bayan bayan gabatar da hujjojin Gwamnan a Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Jihar dake kan Titin Milla, Kano.
Barista Lawan, Wanda yana ɗaya daga cikin lauyoyin da za su kare Gwamnan, ya ce ba buƙatar jam’iyyar PDP ta shigar da ƙara tun da farko, amma tun da har sun riga sun shigar, za su sha zafin faɗuwa.
Ya ce: “Mun kawo hujjojin da za mu kare kanmu da su, kuma mun yi hakan cikin lokaci, kuma muna da ƙarfin guiwar yin nasara, kuma tun farko, muna cewa ba buƙatar PDP ta shigar da ƙara”.
Lauyan ya ce za su kawo shaidu 203 waɗanda manyan shaidu ne, kuma za su faɗa wa Kotun cewa lallai an gudanar da zaɓe, kuma cewa ƙarar da jam’iyyar PDP ta shigar ba ta da tushe.
Lauyan da zai kare Gwamnan ya ce da shigar da ƙarar cikin kwana 20 zuwa 25, za a fara sauraron ƙarar zaɓen gwamnan gadan-gadan.
Ya ƙara da cewa sun shigar da ƙararsu cikin kwana 21 kamar yadda doka ta buƙata, yana mai ikirarin cewa jam’iyyar PDP ba ta shigar da ƙara ba sai da lokaci ya wuce.
“Muna da ƙarfin guiwar yin nasara a wannan ƙarar, saboda duniya gaba ɗaya ta amince an yi zaɓe, kuma haƙiƙa Gwamna Ganduje ya ci zaɓe”, in ji shi.
Lauyan ya yi watsi da jita-jitar cewa su suka sa aka canza wa alƙalan da za su sauri ƙarar wuraren aiki don su kawo waɗanda za su yi musu yadda suke so, ya ce yawan ƙararraki har 50 sun wuce Kotu ɗaya ta saurare su.