An maka Alƙalin Alƙalan Najeriya a kotu

226

Wani ɗan kasuwa ɗan shekara 46, Tochi Michael ya maka Muƙaddashin Alƙalin Alƙalan Najeriya, Tanko Muhammad a wata Babbar Kotun Abuja bisa zargin sa da yin ƙarya wajen bayyana shekarunsa.

A ƙarar mai lamba FCT/HC/BW/CV/79/2019 da aka shigar gaban Kotun tun a watan Afrilu, mai shigar da ƙarar ya ce Alƙalin Alƙalan ya yi ƙaryar shekarunsa da gangan.

Mista Michael ya yi zargin cewa Alƙalin Alƙalan ya yi ƙarya a kwanan watan haihuwarsa daga 31 ga watan Disamba, 1950 kamar yadda yake ƙunshe a dukkan takardunsa har da Takardar Shaidar Kammala Karatunsa ta Sakandare zuwa 31 ga watan Disamba, 1953 lokacin da ya fara aikin shari’a.

Wanda ya shigar da ƙarar yana roƙon Kotun da ta yanke hukunci ko abinda Alƙalin Alƙalan ya yi bai shafi ƙarya, bada bayanan ƙarya da bayan bogi ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan