Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya ta samu sabon shugaba

234

Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya zama Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, NGF.

Gwamnan Ekitin ya yi nasarar zama Shugaban NGF ɗin ne a wani zaɓe da aka gudanar ranar Laraba da yamma a Abuja.

An zaɓi Gwamnan Fayemi a matsayin ɗan takarar da ya fi dacewa ya ƙalubalaci Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, wanda shi ma ya nemi muƙamin.

Gwamna Fayemi zai karɓi shugabanci daga Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan