Rashin tsaro: Masarautar Katsina ta soke hawan Salla

Masarautar Katsina ta bayyana cewa ba za a gudanar da hawan Salla a wannan shekarar ba sakamakon rashin tsaro da ake fuskanta.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sallaman Katsina, Alhaji Bello M. Ifo, Sakataren Masarautar Katsina ya sanyaya wa hannu, wadda aka raba wa manema labarai ranar Juma’a.

“Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji (Dakta)Abdulmumin Kabir Usman, CFR, ya umarce ni da in sanar da al’ummar Jihar Katsina baki ɗaya, cewa bisa ga ibtila’in da ya faɗa wa ‘yan uwanmu Musulmai na yankin Gundumomin Batsari, Ɗan-Musa, Ƙanƙara, Wagini, da dai sauran wuraren da abin ya shafa.

“Don haka Masarautar ta yanke shawarar, ya zama wajibi ta ɗage Hawan Salla, da kuma duk wasu shagulgula don nuna alhininmu ga waɗanda abin ya shafa.

“Amma za a je Sallar Edi kamar yadda aka saba, sannan za a gudanar da addu’o’in zaman lafiya. Muna roƙon Allah Subahanahu Wata’ala ya zaunar da Katsina da ma ƙasarmu lafiya baki ɗaya, amin”, in ji sanarwar.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan