Matsayinmu game da hukuncin Kotun Ƙoli a rikicin APC a Zamfara-INEC

219

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta ce ranar Asabar za ta tattauna don fitar da matsaya game da hukuncin Kotun Ƙoli a rikicin jam’iyyar APC a Zamfara.

Hukumar ta sanar da haka ne a wata sanarwa da Festus Okoye, Kwamishinan INEC kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Ilimantar da Masu Zaɓe ya fitar ranar Juma’a a Abuja.

Mista Okoye ya ce ranar Litinin ta mako mai zuwa ne Hukumar za ta sanar da al’umma matsayar da ta ɗauka.

Ya ce biyo bayan hukuncin da Kotun Ƙolin ta yanke a Abuja game Zaɓen Gwamna, Zaɓen Majalisar Dokoki ta Ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Jiha da aka yi a Jihar Zamfara, INEC ta kira taron gaggawa ranar Juma’a don duba hukuncin Kotun.

“Kotun Ƙolin ta yanke hukuncin cewa jam’iyyar APC ba ta gudanar da zaɓukan fitar da gwani ba kamar yadda doka ta tanada.

“Ta tabbatar tabbatar da cewa dukkan ƙuri’un da jam’iyyar APC ta samu a zaɓukan “ɓatattun ƙuri’u ne”, ta kuma bayyana ‘yan takarar jam’iyyun da suka zo na biyu, kuma suka samu yawan ƙuri’un da ake buƙata, a bayyana su a matsayin waɗanda suka lashe zaɓen.

“Hukumar za ta ƙara tattaunawa gobe Asabar (yau), don ƙara tattaunawa game da batutuwan dake tasowa daga hukuncin, yayinda za a sanar da al’umma matsayin Hukumar na ƙarshe ranar Litinin, 27 ga watan Mayu.

A ranar Juma’a ne Kotun Ƙoli ta yanke hukunci game da rikicin jam’iyyar APC a jihar ta Zamfara, inda ta ce dukkan ƙuri’un da jam’iyyar ta APC ta samu a zaɓen ɓatattu ne, domin kuwa ba ta gudanar da zaɓukan fitar da gwani ba kamar yadda doka ta tanada.

Kotun ta ce jam’iyyun da suka zo na biyu a zaɓen, kuma suka samu yawan ƙuri’un da doka ta tanada su suka ci zaɓen.

Hukuncin dai yana nufin jam’iyyar APC ba ta da ko kujera ɗaya a jihar Zamfara a zaɓukan da suka gabata.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan