Sabon Gwamnan Oyo ya sauke dukkan shugabannin ƙananan hukumomin jihar

253

Sa’o’i kaɗan bayan rantsar da shi, Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya sauke dukkan shugabannin ƙananan hukumomi a jihar.

Shugaban Ma’aikatan Gwamnan, Bisi Ilaka ya sanar da haka a wata sanarwa ranar Laraba a Ibadan.

Gwamnan ya umarci dukkan shugabannin ƙananan hukumomin da su miƙa mulki ga Shugabannin Gudanarwa na Ƙananan Hukumomin ko kuma Daraktoci Mafiya Girma.

Gwamna Makinde ya kuma sa takunkumi a kan asusun ƙananan hukumomin da na Gwamnatin Jihar har sai umarni na gaba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan