Sabon Gwamnan Yobe ya angwance kwana ɗaya bayan ya sha rantsuwar kama aiki

162
Mai Mala Buni
Mai Mala Buni

Kwana ɗaya da ya sha rantsuwar kama aiki, Gwamnan Jihar Yobe, Maimala Buni ya angwance ranar Alhamis.

Gwamna Buni ya angwance ne da Ummi Adama Gaidam, ‘yar gwamna da ya bar gadon mulki, Ibrahim Gaidam.

Amaryar, waddda ke karatu a Saudiyya a halin yanzu za ta kasance matarsa ta uku.

Majiyoyin cikin gida sun ce Mista Buni ne ya nemi Ummi da aure ba tare da sanar da mahaifinta ba tun da farko, don ƙarfafa dangantakarsu ta siyasa.

DAILY NIGERIAN ta gano cewa an yi bikin auren nasu ne a gidan tsohon Gwamna Gaidam wanda ke yankin Sabon Fegi a Damaturu, babban birnin jihar.

“An raba goro jiya, an kuma ɗaura auren yau a gaban wasu iyalai ‘yan kaɗan” in ji wata majiya da ta buƙaci a sakaye sunanta.

Mista Buni shi ne Sakataren Jam’iyyar APC mai mulki kafin ya zama Gwamna, kuma Mista Gaidam ne ya nuna shi don ya gaje shi a matsayin Gwamna.

Mai Shari’a Garba Nabaruma ne ya rantsar da Gwamnan jiya Laraba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan