APC ta ɗauki mataki na ƙarshe a kan tsohon Gwamnan Zamfara

210

An kori tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari daga jam’iyyar APC sakamakon ƙaddarar faɗuwa zaɓe da ta samu jam’iyyar a jihar.

Tuni dai Kotun Ƙoli ta soke dukkan ƙuri’un da jam’iyyar ta APC ta samu a zaɓen da ya gabata, inda Kotun ta ce APCn ba ta gudanar da sahihan zaɓukan fitar da gwani ba kamar yadda doka ta tanada.

Hakan ne yasa jam’iyyar ta APC ta rasa gwamna, ‘yan majalisun jihar, ‘yan Majalisar Wakilai da sanatoci a jihar.

Bayan hukuncin na Kotun Ƙoli, sai Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta bayyana jam’iyyar da ta zo ta biyu a zaɓen, PDP a matsayin wadda ta yi nasara.

An kori Mista Yari ne tare da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APCn na Ƙasa (Arewa), Lawali Shuaibu.

Ana zargin mutanen biyu da yi wa Babban Kwamitin Zartarwa na Ƙasa na Jam’iyyar ƙafar angulu lokacin gudanar da zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar a jihar.

An ɗauki matakin korar tsohon Gwamnan da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa ne a ƙarshen wani taron tattaunawa na gaggawa da aka yi a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Wata sanarwa da Shugaban Jam’iyyar na Jihar Zamfara, Surajo Maikatako da Sakataren Yaɗa Labarai, Muhammad Bakyasuwa suka sanya wa hannu ta ce an kore su ne sakamakon “Yari da abokan tafiyarsa sun kunyata jam’iyyar a jihar Zamfara.

“Tsohon Gwamnan ya yi ƙafar angulu ga ƙoƙarin jam’iyyar na gudanar da zaɓen fitar da gwani a bara, hakan ne yasa ta haifar da ƙaddarar faɗuwa zaɓe da ta samu ta a jihar”, a cewar wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar.

“Bayan duba yadda jam’iyyarmu ta samu kanta a babban zaɓen da ya gabata da kuma hukuncin Kotun Ƙoli, mun kori tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Lawali Shuaibu daga jam’iyyar APC.

Biyo bayan wannan ci gaba, muna buƙatar su da cikin gaggawa su miƙa dukkan kayayyakin jam’iyyar da suke hannunsu, har da kuɗaɗe.

“Yari da yaransa sun lalata yunƙurin shelkwatarmu ta ƙasa na gudanar da zaɓukan fitar da gwani ranar 3 da 7 ga watan Oktoba, 2018. Munanan abubuwan da ya yi suka haifar da mutuwar mutum shida, aka kuma jikkata fiye da 200.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan