Wata Babbar Kotun Tarayya dake zamanta a Abuja ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC da ta ba Rochas Okorocha, tsohon Gwamnan Jihar Imo Takardar Shaidar Cin Zaɓe a matsayin Sanata da zai wakilci Imo ta Yamma.
Mai Shari’a Okon Abang na Babbar Kotun Tarayyar ya yanke hukuncin cewa tunda dai Baturen Tattara Sakamakon Zaɓe ya bayyana Okorocha a matsayin wanda ya lashe zaɓen 23 ga watan Fabrairu na Mazaɓar Sanata ta Imo ta Yamma, babu dalilin da INEC za ta ƙi ba shi Takardar Shaidar Cin Zaɓensa.
Kotun ta yanke hukuncin cewa matakin da INEC ta ɗauka na hana Okorocha Takardar Shaidar Cin Zaɓe “mataki ne da doka ba ta yadda da shi ba”.
Alƙalin ya tabbatar da cewa Baturen Tattara Sakamakon Zaɓe na INEC ne kaɗai yake da dama a bisa tsarin mulki ya bayyana wanda ya lashe zaɓe.
Ya tabbatar da cewa duk wani mutum da Baturen Tattara Sakamakon Zaɓe ya bayyana a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaɓe, zai ci gaba da kasancewa a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaɓe har sai masu ƙara sun yi nasarar kawar da wannan nasarar a Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓe.
INEC ta ce ta ƙi ba Okorocha Takardar Shaidar Cin Zaɓe ne bayan Baturen Tattara Sakamakon Zaɓe na Mazaɓar Sanata ta Imo ta Yamma ya ce tilasta masa aka yi ya bayyana Okorocha a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaɓe.
Da yake mayar da martani game da hukuncin Kotun ranar Juma’a a Owerri, babban birnin Jihar Imo, tsohonan ya ce duk abinda ya faru game da Takardar Shaidar Cin Zaɓensa abu ne da yake cikin tsarin Ubangiji, don dimukuraɗiyyar ƙasar nan ta ƙarfafa, an kuma kare haƙƙin ‘yan ƙasa duba da yadda kotun ta yanke hukunci bisa riƙe Takardar Shaidar Cin Zaɓensa.
Okorocha ya ce ya yafe wa Farfesa Innocent Ibeabuchi, Baturen Tattara Sakamakon Zaɓen Sanata na Imo ta Yamma, wanda ya yi iƙirarin cewa ya bayyana shi a matsayin wanda lashe zaɓen ne bisa tilas, da kuma dukkanin waɗanda suka taka rawa wajen wahalar da ya sha bisa Takardar Shaidar Cin Zaɓen tasa.