Takarar Shugaban Majalisar Dattijai: Gwamnonin APC sun bayyana wanda suke goyon baya

192

Gwamnonin Jam’iyyar APC sun goyi bayan takarar Jagoran Majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawan da Jagoran Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamia don yin shugabancin Majalisar Dokoki ta Ƙasa Zubi na 9.

Gwamnonin ƙarƙashin tutar Ƙungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC, sun ɗauki matakin ne a wani taron ganawa na sirri da aka yi a Gidan Gwamnan Kebbi dake Abuja ranar Lahadi da daddare.

A lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi bayan kammala taron, Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu, wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin na Jam’iyyar APC ya ce gwamnonin sun ɗauki matakin ne don yin biyayya ga umarnin shugabancin jam’iyyar na ƙasa.

Ya yi amfani da da wannan dama ta taron ganawar, wanda shi ne Irin sa na farko tun bayan da aka kammala babban zaɓen ƙasar nan wajen yin maraba da sabbin gwamnonin da suka shigo ƙungiyar.

Gwamna Bagudu ya roƙi dukkan ‘yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa na Jam’iyyar APC da su zaɓi shugabanni biyu, yana mai cewa Ƙungiyar Gwamnonin tana goyon bayan matakin jam’iyyar ɗari bisa ɗari.

Ya ƙara da cewa Ƙungiyar ta yi imanin cewa shugabancin jam’iyyar ya ɗauki matakin da ya dace da suka ce a zaɓi Sanata Lawan da Gbajabiamia a matsayin shugabanni.

Ya kuma ce gaba ɗaya Gwamnonin APCn suna goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin Jagoran Jam’iyyar, yana mai tabbatar da cewa za su yi aiki tare da shi don kai ƙasar nan ga Mataki na Gaba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya ruwaito cewa waɗanda suka halarci taron tattaunawar sun haɗa da gwamnonin jihohin Edo, Kwara, Kogi, Plateau, Nasarawa, Kano, Jigawa, Ekiti, Osun da Lagos.

Sauran sun haɗa da gwamnonin jihohin Gombe da Niger da Mataimakan Gwamnonin Borno da Kaduna.

NAN ya ce sai dai ba a ga ƙeyar gwamnonin jihohin Katsina, Ogun, Ondo da Kebbi ba a yayin taron ganawar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan