Matsalar fyaɗe matsalace da ta shafi zamankewar rayuwar ɗan- Adam duba da yadda ake samun ƙaruwar matsalar a cikin al’umma, haka yana zama koma baya ta fannoni daban-daban duba da yadda ake samun karuwar fyade na yara ƙanana. Yaran da matsalar ta fi shafa su ne waɗanda ba su wuce shekara biyu zuwa bakwai ba, wanda waɗannan shekaru, shekaru ne na yara wanda ba su san komai ba duba da yadda ake musu wayo da abin kwaɗayi ko tsoratarwa da makami ko bulala ko wani abu dai na bada tsoro, wanda yaran za su razana ko amfani da ƙarfi wajen biyan buƙata. Kuma waɗannan shekarun daga shekara biyu zuwa shekara bakwai, shekaru ne da yara suke shiga cikin matsala idan aka samu rabuwar aure, to haka yaran za su tashi babu kulawa da kuma aiken su ko ina da rashin kula da al’amarinsu.
Abubun da suke kawo fyaɗe:
*Attraction/ ɗaukar hankali na mace da ta fito da surar jikinta, haka yana sa namiji fita daga cikin hayyacinsa domin aikata fyaɗe.
Samun dama na keɓewa da mace, wanda hakan yana iya kawo fyaɗe a tsakanin al’umma.
*Curiousity/ neman sanin mace, wanda ya haɗa da amfani da ƙarfi ko kuma razanarwa.
*Inadequate socialization/ rashin sanin menene matsalar fyaɗe ko hukuncinsa ga masu aikata ɗabi’ar.
*Kallan fina-finan da ba su yi dai-dai da al’adunmu ba ko addininmu, ita ma wannan wata hanya ce ta koyar da ɗabi’a mara kyau.
*Personality disorder/ wani hali da mutun yake dashi na rashin da’a ko rashin bin doka.
*Mental illness/ rashin lafiyar da ta shafi tunani ko zuciya takan sa ɗan-Adam aikata abinda ba dai-dai ba. Barin marasa lafiya waɗnda rashin lafiyarsu ta shafi ƙwaƙwalwa cikin al’umma shi ma yana kawo fyaɗe tunda ai suma suna da sha’awa.
Matsalar fyaɗe na ɗaya daga cikin manyan matsalalon da suke ci wa al’umma tuwo a ƙwarya. A koda yaushe, kowane lokaci ka kunna kafar yaɗa labarai za ka ji ana shirye-shirye na wayar wa da al’umma kai akan matsalar, amma kullum ƙara ci gaba take kamar wutar daji. Kuma yanzu abin mamakin ma a ko ina ana iya samu. Babban mutun ya yi wa yarinya fyaɗe a unguwanni, kasuwanni, makarantu da sauran guraren gudanar da rayuwa.
A kwanakin baya kaɗan an samu wani mutun ya yi wa yarinya ‘yar wata shida fyaɗe, wannan ba ƙaramin zalunci ba ne. Idan aka yi duba da kyau, wane dalili ne ya sa shi hakan? Abu biyu ne zai iya faruwa kodai ya yi ne dan cin zarafi kawai ko kuma yabi umarnin zuciyarsa ta ɗora shi a keken ɓera cewa idan ya yi amfani da yarinya wadda ba ta cika shekara ɗaya ba zai samu wata waraka. To yanzu idan ya yi hakan ne dan wata biyan buƙatarsa, yanzu an yi biyu babu, ya zalunci ‘yar mutane, shi kuma kotu ta yi masa hukunci.
Fyaɗen da yake faruwa na matasa ya sha bamban da wanda yake faruwa na manyan mutane da ake samu da laifin fyaɗe. Idan muka kalli ta manyan da ake kamawa da laifin fyaɗe da yawa yana faruwa wajan dama suna da ɗabi’ar tun yarintarsu, ko kuma bayan girma ya zo musu su ɗauki ɗabi’ar. Wasu suna komawa kamar ƙananan yara saboda sha’awa su ji suna da sha’awa kamar yara masu tasowa.
Wasu kuma haka yana faruwa ne sakamakon rashin samun gamsuwa daga wajan matansu tunda mace tana daina sha’a, namijin kuma ba ya dainawa, lokacin kuma ba ya tunanin sake wani auren da zai samu nutsuwa ko biyan buƙata, wannan wani abu ne da yake kawo fyaɗe a tsakanin manyan mutane.
Daga
Shuaibu Lawan
shuaibu37@gmail.com
08037340560 (Saƙo kawai)
Kyakkyawan post
Good post 🙂