Wani malamin sakandire a Kano ya kashe kansa

151

Femi Oguntumi, wani malamin Karish College dake Kawaji a yankin Ƙaramar Hukumar Nasarawa ta Jihar Kano ya kashe kansa da kansa.

DAILY NIGERIAN ta gano cewa mamacin, wanda ɗan asalin Jihar Ondo ne ya rataye kansa ne a jikin fankar sama dake ɗakinsa ranar Juma’a.

Rahotanni sun ce an gano gawar Mista oguntumi ne lokacin da abokinsa ya zo neman sa a gidan da yake da zama, sai abokan hanyarsa suka ɓalle ƙofar ɗakinsa, suka same shi matacce, jikinsa yana wari.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta tabbatar da faruwar wannan al’amari ranar Juma’a, ta bakin mai magana da yawunta, Abdullahi Haruna.

Mista Haruna ya ce al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na dare, ya ƙara da cewa tuni aka kai gawar mamacin Ɗakin Ajiye Gawarwaki na Asibitin Ƙwararru na Murtala Mohammed.

Tuni Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta fara bincike don gano dalilin da yasa Mista Oguntumi ya kashe kansa.

Mista Haruna ya ce Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, Iliyasu Ahmed ya bada umurnin gudanar da cikakken bincike don gano dalilin da yasa Mista Oguntumi ya kashe kansa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan