Rayuwar mata ta ƙara samun koma-baya a Jihar Kano, duba da yadda ƙididiga ta bada, akwai mata sama da milyan ɗaya da aurensu ya mutu, muna magana ne akan wanda sukayi rijista ne kawai da Ƙungiyar Zawarawa ta Jihar Kano. Domin in ana maganar zawarawa ana magana ne da wanda suka rasa mazansu ta hanyar rasuwa, amma a nan ana maganar waɗanda aka saki ne kawai.
Kowace al’umma tana da doka ta zamantakewa, zamantakewa ta haɗa da tsara doka a harkar auratayya da al’ada (Culture), da kuma addini (Religion). Kowane ɓangare a ko wacce al’umma akwai, sai dai ba haka abin yake ba a Jihar Kano. Bincike ya tabbatar da Arewacin Najeriya shi ne yankin da ya fi kowane yanki yawan al’umma, kuma shi ne yanki da ake samun ƙaruwar mutuwar aure, musamman Jihar Kano. Ita ce jihar da ta yi shura wajan wannan babbar matsala da take damun al’umma ko ci musu tuwo a ƙwarya, kuma abin mamakin kaso 95 cikin ɗari na al’ummar Kano Musulmi ne. To ina matsalar take? Bari mu ɗan yi nutso a ilimin Sociology, domin gane ina matsalar take, ko ya ta samu asali, amma kafin wannan dole mu tambayi kanmu wadata ce take kawo mutuwar aure ko talauci?
Da yawa masu ilimi sun tafi akan talauci ne yake kawo mutuwar aure, haka ma yana faruwa, amma tunanina ko nazarina ya sha ban-ban da wancen nazarin, duk da ni ma na yarda da hakan, amma akwai wasu abubuwan da suke ƙara kawo matsalar, in muka kalli yadda tsarin aure yake a baya ko dokar al’ada a ƙasar Hausa. Domin a bayan ai akwai talauci amma sakin aure yana zama abin kunya a baya. Yanzu wani zamani muka keto na iyaye wakilcin aure kawai suke yi, ba sa kula da al’amarin auren. Wannan yana daga cikin abinda yake rusa aure, sai na gano aro al’adar da ba ta dai-dai da al’umarmu ba a auratayya, kowa so yake sai ya yi ‘fashion’ a aure koda ƙarfin tattalin arziƙinsa ya kai ko bai kai ba.
Kaso 80 cikin ɗari na matasa suna aure ne dan biyan buƙatar sha’awarsu, ba su da cikaken sanin mene ne ilimin auren, me yasa ake yin aure, zaman namiji shugaba ba shi ne yake nuna mace ta zama baiwa ba ko mara daraja. Ana gina aure ne ta fannin ƙauna da soyayya da amincewa zama waje ɗaya har tsawan rayuwa. Me yasa wannan soyayyar da ake yi take ƙarewa ƙasa da wata huɗu.
Wannan nauyi ne akan kowa, a dawo da Dokar Aure, in kuma babu ita to lallai a dawo da ita, idan aka bari wannan matsalar ta ci gaba to lalle zuwa wani lokaci za ta mamaye kowane gida a Jihar Kano, a ba wa al’umma ilimin zamantakewar aure, a samu manya a kowane gida su ne za su kula da harkar aure, duk abinda ya faru a yi maza a je a gyara shi domin gudun mutuwar aure.
Daga
Shuaibu Lawan
shuaibu37@gmail.com