Wassu tsaffin jami’an gwamnatin Jihar Gombe ta Ibrahim Hassan Dankwambo, sun zargi Kwamitin Bincike da Ƙwato Kadarori da ake zargin an rabar ba bisa ka’ida ba wadda Gwamna Inuwa Yahaya ya kafa, da yin kama karya da yi wa doka karan-tsaye wajen gudanar da aikinsa.
Tsohon Kwamishinan Shari’a a Gwamnatin ta Dankwambo, Barista Muhammad Umar Mailumo ne ya yi zargin ranar Litinin ɗin nan yayin wani taron manema labarai a Gombe.
Yace sayar da kadarori da tsohuwar gwamnatin ta yi wa jami’anta abu ne da bai saɓa wa doka ba.
“Dokar da ta bada damar yin haka ba ma Gwamnatin Ibrahim Hassan Dankwambo ba ce ta kafa ta, dokar tana nan tun zamanin Gwamna Goje, kuma duk wadda yasan tsarin aikin gwamnati yasan ana yi wa motar jami’i kuɗi ya biya ta zama mallakinsa a yayin da ya gama aiki, wannan ba wani sabon abu ba ne.” a cewar Barista Mailumo.
Ya kuma zargi Kwamitin da yin amfani da karfin jami’an tsaro wajen kwato kadarori daga jami’an tsohuwar gwamnatin, yana mai musanta cewa wai suna mayar da kadarorin ne da karan kansu, tare da zargin Kwamitin da yin karan-tsaye ga doka, yana mai cewa sun shigar da kara ƙalubalantar sahihancinsa a gaban kotu.
Tsohon kwamishinan ya zargi gwamnatin ta Inuwa da yin amfani da kwamitin don cin zarafin tsaffin jami’an gwamnatin da ta gabata.
Ya kara da cewa: “Wannar gwamnati ba abinda ta sa a gaba sai ƙoƙarin muzguna wa waɗanda suka yi aiki da Dankwambo, ta ƙi ta mayar da hankali kan alhakin da talakawa suka ɗora mata, ta koma cin mutunci da karya doka. To amma, ay i dai mu gani.”
A kwanan nan ne dai sabuwar gwamnatin ta Inuwa Yahaya ta kafa wani kwamiti mai mambobi 7 da nufin ƙwato kadarorin gwamnati da take zargin tsohuwar gwamnatin ta Dankwambo ta raba wa jami’anta ba bisa ka’ida ba, waɗanda suka haɗa da motoci da filaye da KEKE NAPEP da dai sauransu.