Ranar Yan Gudun Hijira Ta Duniya

188


A duk shekara, dubun dubatan mutane suna barin muhallan su bisa wasu dalilai domin neman mafaka a wasu wurare. Wadannan dalilai sun hadar da yake- yake, da Annoba, da talauci, da Fari, da barkewan cututtuka ko gudun hukunci na zalunci, da dai sauransu.

Hakan ya sa Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 2001 ta ware ranar 20 ga watan Yuni kowacce shekara domin gudanar da bikin Yan Gudun hijira a duniya.

A bana, an samu kasashe sama da 100 da suka gudanar da bikin a fadin duniya waanda ya hada da ma’aikatan gwamnati, da kungiyoyin agaji, da fitattun mutane, da yan Gudun hijira da sauran al’umma baki daya.

Wani kididdiga na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa a kowanni minti daya, ana samu mutum 25 da suke gudun hijira daga muhallansu. A kasarnan, kididdiga ya nuna cewa akwai yan gudun hijira mutum miliyan biyu a bangarori daban-daban, sannan akwai wasu dubu 239,000 a makwabtan kasashe.

Taken bikin na bana shi ne samar da taimako ga mutane masu gudun hijra saboda mawuyacin hali da sukan tsinci kansu a mafi yawancin lokuta a sansanin da suke zaune.

Duk da cewa akan yi sa a wasu sansanin sukan wadatu da abubuwan more rayuwa kamar ruwan sha mai kyau, da abinci, da sutura, da makwanci, da makaratun, da asibitoci, da wutan lantarki da dai sauraru.

Amma a lokuta da dama yan gudu hijira sun fi samun kansu cikin bukatan wadannan abubuwa a sansanin da suke zaune. Don haka bikin na bana ya ke jan hankali al’umma zuwa ga taimakawa yan gudun hijira a sansaninsu domin inganta rayuwarsu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan