Mata Masu Ciki Da Dama Na Mutuwa Yayin Haihuwa- UNPF

210

Majalisar Dinkin Duniya (United Nations) ta ce mata masu ciki da dama na rasa rayukansu yayin haihuwa duk da irin kudaden da gwamnatin kasarnan ke kashewa don ganin ta magance hakan.

Hukunar kula da kidayar al’umma reshen majalisar (UNITED NATIONS POPULATION FUND) ta ce akalla ana samun mata 110 da ke mutumwa kullum sanadiyyar haihuwa ko matsalolin ciki a kasarnan.

Shugaban reshen UNPF, madam Maryama Darboe ce ta bayyana hakan yayin gabatar da sakamakon binciken da kungiyar kula da lafiyar mata masu juna biyi ta dauki nauyin gudanarwa.

Madama Maryama ta ce har yanzu fiye da shi 80 cikin 100 na mata a kasarnan na cigaba da dogaro da haihuwa a gida a madadin zuwa asibiti wanda hakan ya fi yawa a tsakanin matan Arewacin Kasarnan.

Ta kara da cewa gwamnati na kashe kudade kimanin naira tiriliyon daya duk shekara a fannin lafiya don ganin an magance mutuwar mata wurin haihuwa kamar yadda kudurin Majalisar Dinkin Duniya ya tanada.

A nata bangaren, shugabar kungiyar wayar da kai ta kasa, Hajiya Saudatu Sani ta bayyana rashin jin dadin ta dangane da gazawar gwamnonin jihohi a fannin kula da lafiyar mata masu ciki.

A karshe, hajiya Saudatu ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a fannin, da su tabbatar da sun samar da tsare-tsare da zai magance hakan, tare da fadakar da ma’aurata alfanun tazarar haihuwa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan