Zamu Samar Da Ilimi Kyauta Inji Gwamna Fintiri

210

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya ce gwamnatinsa za ta cire biyan kudin makaranta a makarantun gwamnati da ke jihar.

Gwamnan ya bayyana haka a lokacin da yake karbar bakuncin dan takarar gwamna a zaben da ya gabata karkashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) sanata Abdulaziz Nyako a lokacin da ya kai mai ziyara ta musamman.

Gwamnan ya ce daga watan satumba shekarar nan, dalibai da ke karatu a makarantun gwamnati a jihar zasu daina biyan kudin makaranta domin tabbatar da tsarin samar da Ilimi kyauta ga al’umma.

Daga nan Gwamna Ahmadu ya kara jaddada alkawarinsa na samar da ilimi ga dukkanin yara a jihar musamman wanda suke fama da talauci.

Gwamna Fintiri ya kara da cewa gwamnatinsa tuni ta fara ciyarwa a makarantu kyauta a kauyuka kuma tana yunkurin cigaba da ciyarwan a dukkanin makarantun gwamnati domin bunkasa harkar ilimi a jihar.

Daga karshe, gwamnan ya kara da cewa burinsu shi ne makarantun gwamnati su yi gogayya da makarantu masu zaman kansu a fanin ingancin ilimi.

A nasa bangaren, sanata Abdulaziz Nyako ya ce a shirye suke su bawa gwamnati goyon baya ga tsare-tsaren ta don samar da cigaba a jihar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan