Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Zamfara ba ta samu ƙarancin alhazai da za su je aikin haji na bana sakamakon tashin hankalin da ake fama da shi a jihar.
Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar, Abubakar Sarkin-Pawa ya bayyana haka ranar Alhamis a Abuja.
Ya ce matsalolin tsaro sun shafin yawan maniyyata da za su aikin hajin bana daga jihar.
“E, matsalolin tsaro sun shafi yawan fitowar alhazai daga Zamfara saboda idan za ku iya tunawa, a 2016, mun samu alhazai 5,000 daga Jihar Zamfara, a 2017 kuma, mun yi jigilar alhazai 4,000.
“Yanzu mun dawo ƙasa, muna da alhazai 1,500 ne. Kun san yawancin mutanen dake biyan kuɗinsu na aikin haji Fulani ne makiyaya, kuma kaso mai tsaka daga cikinsu na zuwa ne daga ƙauyuka, kuma waɗannan matsalolin tsaro sun shafe su”, in ji Mista Sarkin-Pawa.
Shugaban Hukumar ya ce Gwamnatin Jihar ta tabbatar da cewa an samar da isasshen tsaro don tabbatar da tsaron alhazai a ciki da wajen sansanin alhazai dake Gusau, babban birnin jihar.
“Kun san sansanin alhazanmu yana tsakiyar Gusau, kuma kun san Gusau tana da tsaro saboda ba ta taɓa samun wani hari ba daga mahara.
“Mukan yi aiki da hukumomin tsaro da suka dace kamar Rundunar ‘Yan Sanda, Rundunar Sojoji da sauran hukumomin tsaro, Gwamnatin Jihar tana tallafa musu don su raka alhazanmu har daga sansani zuwa filin jirgi”, in ji shi.
Ya ce Hukumar ta tuntuɓi Majalisar Malamai don ta ilmantar da alhazan game da yadda ya kamata su yi halayyar kirki a yayin da suke a Ƙasa Mai Tsarki.
“Koda yake dai, alhazanmu masu bin doka ne saboda ba mu taɓa samun wata matsala da su ba”, a kalamansa.
Ya ƙara da cewa aikin hajjin 2019 ya samu gagarumin ci gaba idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.
“Muna ƙoƙarin sauƙaƙa aikace-aikacen haji kowace shekara, mun yi nazarin abinda ya faru a 2018 muka shigo da wasu canje-canje a aikin hajin 2019.
“Daga cikin canje-canjen da muka shigo da su shi ne za mu buga biza a ofishinmu na jiha ba sai mun ɗauke da mun kai Kano, Kaduna ko Legas ba”, a cewar Mista Sarkin-Pawa.