Masu ruwa da tsaki a jigilar alhazan bana sun bayyana irin shirin da suka yi don fara jigilar alhazai

122

A jiya Alhamis ne masu ruwa da tsaki a jigilar alhazan bana suka bayyana irin shirin da suka yi gabanin fara jigilar alhazai zuwa Ƙasa Mai Tsarki ranar 10 ga watan Yuli, suna masu cewa an kammala shirye-shirye tsaf don fara jigilar cikin nasara.

Masu ruwa da tsakin sun bada wannan tabbacin ne a wani taron ganawa na Kwamitin Aiki na Masu Ruwa da Tsaki da Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, Shiyyar Arewa Maso Yamma ta shirya gabanin fara jigilar alhazan ranar 10 ga watan Yuli.

Da yake tattaunawa da manema labarai, Shugaban Shiyyar Arewa Maso Yamma na NAHCON, Lawan Ahmad ya ce maƙasudin taron ganawar shi ne a yi musayar ra’ayi da manyan masu ruwa da tsaki domin jin irin shirin da suka yi gabanin fara jigilar alhazan.

Ya bayyana gamsuwa da irin shirin da masu ruwa da tsakin suka yi, yana mai kira gare su su ci gaba da yin haka har zuwa ƙarshen jigilar alhazan bana.

Ya ce za a ƙaddamar da jigilar alhazan ne da maniyyatan Jihar Katsina, yayinda na Jihar Kano za su fara tashi ranar 11 ga watan na Yuli.

Shugaban ya yi kira ga alhazan da su zama masu kiyaye doka da oda, su kuma sa a ransu cewa za su gudanar da ɗaya daga cikin Rukunan Musulunci ne.

Daga nan sai Mista Ahmad ya yi kira ga alhazan da su yi wa ƙasar nan addu’ar zaman lafiya da ci gaba.

A jawabinsa tun da farko, Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, Mai Kula da Aikace-aikace, Abubakar Shika ya bayyana cewa Rundunar ‘Yan Sandan ta ɓullo da sabbin dabarun tsaro waɗanda za a yi amfani da su kafin, lokacin da bayan kammala jigilar alhazan.

Daga ƙarshe ya yi kira ga NAHCON da ta ba Rundunar jadawalin jigilar alhazan don bada kulawar da ta dace idan buƙatar gaggawa ta taso.

A ɓangarensa, Shugaban Sashin Aikace-aikacen Filayen Jirgi na Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Ƙasa, FAAN, Muhammad Bello ya ce an tanadi injina da suka haɗa da kyamarorin sirri da kayayyakin tantancewa don gano duk wani mugun aiki da aka son aikatawa a filayen jirgin.

Ya kuma ƙara bayyana cewa ma’aikatan filayen jirgi suna cikin shiri ko-ta-kwana don yin maganin mutane masu jefa wa matafiya muggan ƙwayoyin a jakunkuna, abinda ke jefa su cikin tsari, yana mai cewa tuni sun kawo ƙarshen wannan mummunan aiki.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan