Karanta rahoton masana yanayi na yau Juma’a

146

Hukumar Hasashen Yanayi ta Ƙasa, NiMet ta yi hasashen cewa za a samu tsawa da ruwan sama a faɗin ƙasar nan ranar Juma’ar nan.

Rahoton yanayi na NiMet na ranar Alhamis ya yi hasashen samun yanayin gajimare da yiwuwar samun tsawa a jihohin Sokoto, Katsina da Kano dake Arewacin Najeriya ranar Juma’a da safe.

A cewarta, ana sa ran samun tsawa a layukan Kano da Yelwa, yayinda ake sa ran sauran sassa su samu yanayin gajimare a ranar Juma’ar.

Ta kuma ƙara yin hasashen cewa yanayin zafi da sanyi a Arewacin ƙasar nan zai kai digiri 29 zuwa 32 a ma’aunin Celcius.

“A jihohin tsakiya, akwai yiwuwar samun tsawa a Abuja, Naija, Plateau, Adamawa da Taraba, yayinda ake sa ran samun yanayin gajimare a sauran sassa a safiyar Juma’ar.

“Bayan nan kuma a ranar Juma’ar dai, ana sa ran samun tsawa a gaba ɗayan yankin da yanayin zafi da daddare zai kai digiri 22 zuwa 31 da kuma digiri 16 zuwa 24 a ma’aunin Celcius”, in ji rahoton na NiMet.

Ta ƙara da cewa a jihohin Kudu, akwai yiwuwar samun ruwan sama tsaka-tsaki a yankin dake da jihohi kamar Osun, Ado da Enugu, yayinda ake sa ran samun gajimare da safe.

Za kuma a samu ruwan sama tsaka-tsaki a yankin yayinda yanayin sanyi da zafi na dare da rana zai kai digiri 27 zuwa 30 a ma’aunin Celcius, da kuma digiri 21 zuwa 24 a ma’aunin na Celcius.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan