Za mu yi tsayuwa irin ta daka wajen warware matsalolin ilimin Najeriya- Ahmad Lawan

159

Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmad Lawan ya bayyana shirin Majalisar Dattijai ta 9 na ƙirƙirar manufofi da dokoki da za su gyara ɓangaren ilimin ƙasar nan.

Mista Lawan ya sanar da haka ne a yayin wata liyafar cin abincin dare da Tsaffin Ɗaliban Makarantar Sakandiren Gwamnati ta Gashuwa suka shirya ranar Laraba a Abuja.

Wata sanarwa da Mataimakinsa na Musamman Kan Kafafen Watsa Labarai, Mohammed Isa ya fitar ta ce waɗannan gyare-gyare za su taimaka wajen dawo da kimar ilimin ƙasar nan da ta riga ta zube.

Ya bayyana rashin jin daɗi bisa irin halin da makarantun firamare da sakandire da manyan makarantun gwamnati ke ciki na rashin isassun kayayyakin more rayuwa, rashin malamai da suka cancanta da kuma manhaja.

Daga nan sai Mista Lawan ya ce dole a dawo da kimar makarantun gwamnati, a kuma tabbatar da ɗorewar haka.

Idan ana so Najeriya ta ci gaba, ya ce dole a fifita manufar ilimi mai inganci.

“Dole mu farka daga baccin da muke yi, mu kuma tabbatar da cewa tsarin koyarwarmu ya zama karɓaɓbe ga kowa. Gine-ginen makarantumu sun yi nisa sosai da ƙalubalen duniya ‘yar yayi.

“Dole mu tashi mu fuskanci wannan yanayi. Akwai abubuwa da yawa a gabanmu idan muna so al’umma ta yi mana adalci. Wannan Majalisar Dattijan za ta fito da wani tsari inda za mu sa wani wa’adi da muke so mu cimma buƙatunmu.

“Muna alfaharin kasancewa waɗanda suka yi makarantar gwamnati, tun daga makarantun firamare har jami’a. Amma me za mu iya cewa a waɗannan kwanaki na zamani duba da mummunan yanayin da kayayyakin more rayuwa ke da ingancin waɗannan makarantu?

“Samar da hanyar samun ilimi mai daidaito mai inganci shi ne abinda za mu fi mayar da hankali a Majalisar Dattijai ta 9 kai da ma Majalisar Dokoki ta Ƙasa gaba ɗaya”, in ji sanarwar.

A tsokacinsa, Shugaban Ƙungiyar, Farfesa Abdulqadir Shettima ya yaba wa Majalisar Dattijan bisa yadda suka amince da shugabancin Shugaban Majalisar Dattijan.

Saboda haka sai ya tabbatar da cewa ‘yan Najeriya ba za su ji kunya ba da zaɓen Mista Lawan a matsayin Shugaban Majalisar Dattijai.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan