Gwamna Zulum ya kai ziyarar bazata a wasu asibitocin Maiduguri

226

A tsakar daren Litinin ɗin da ta gabata ne Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya kai ziyarar bazata ga asibitoci da wasu hukumomin gwamnati a Maiduguri.

Mista Zulum, wanda ya je Umaru Shehu Ultra Modern Hospital da misalin ƙarfe 1:00 na dare bai samu ko likita ɗaya a bakin aiki ba.

Ma’aikatan jiyya 10 kaɗai daga cikin ma’aikatan jiyya 135 dake aiki a asibitin ke kan aiki; yayinda babu wani likita mai neman ƙwarewa daga cikin likitoci masu neman ƙwarewa 19 na asibitin da yake bakin aiki.

Gwamna Zulum ya kira kimanin likitoci 10 a waya don ya ji me yasa ba su zo aiki ba, amma ba su amsa kiran nasa ba.

Amma Asibitin Ƙwararru na Jihar, gwamnan ya samu wasu likitoci kaɗan dake bakin aiki da misalin ƙarfe 2:00 na dare.

Gwamnan ya bayyana rashin jin daɗinsa bisa ingancin kulawar da ake ba marasa lafiya dake kwance.

Ya aika wa Shugaban Umaru Shehu Ultra Modern Hospital takardar neman bahasi don ya yi bayanin me zai hana ba za a ladabtar da likitocin da ba su zo aiki ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan