Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya umarci kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da suci gaba da zama a jahar Kaduna domin ci gaba da daukan atisaye bayan sun lashe gasar Aiteo a karshen makonnan.
Hakan ya biyo bayan kungiyar kwallon kafan ta Kano Pillars zata buga gasar zakarun nahiyar Afrika da a ranar 10 ga watan Ogusta mai kamawa da kungiyar kwallon kafa ta Asantika Toko dake kasar Ghana.


Inda aka bayyana cewar sai ranar 5 ga watan Ogusta zasu dawo gida Kanon Dabo.
Turawa Abokai